Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-03 16:58:32    
Mutum-mutumin sassaka na Dazu

cri

Da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan mutum-mutumin sassaka na Dazu, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin musamman mai lakabi haka 'kogunan dutse na Mo Gao'.

Mutum-mutumin sassaka na Dazu suna da nisan kilomita 163 a tsakaninsu da birnin Chongqing, wanda aka mayar da shi a matsayin birni ne da ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kai tsaye a watan Maris na shekarar 1997. Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi mutum-mutumin sassaka na Dazu a cikin takardar sunayen tsoffin kayayyakin tarihi na duniya a watan Disamba na shekarar 1999 da ta gabata. An fara sassaka mutum-mutumi tun daga shekarar 892 har zuwa karshen zamanin daular Song ta Kudu ta kasar Sin, an dauke shekaru fiye da 250 ana sassaka. Mutum-mutmin sassaka na Dazu kayayyakin sassaka ne masu nagarta a kasar Sin.

An sassaka mutum-mutumi fiye da 50,000. Wadannan mutum-mutumin da aka fi samunsu a cikin tudun Arewa da na Baoding da na Kudu sun jawo hankulan mutane saboda girmansu da kyaun ingancinsu da kuma abubuwan da suka shafa. A shekarar 1961, hukumar wurin ta mayar da mutum-mutmin sassaka na Dazu a matsayin muhimman kayayyakin tarihi na rukuni na farko da dole ne ta kiyaye su.

Muhimmancin mutum-mutumin Dazu ya yi daidai da na sauran shahararrun kogunan duwatsu da ke Dunhuang da Yungang da Longmen da ke arewacin kasar Sin.

Yawancin mutum-mutumin da aka sassaka suna da nasaba da addinin Buddha, shi ya sa ana kiransu littafi mai tsarki na kasashen Gabas da aka sassaka cikin duwatsu. Ko da yake haka ne, an sassaka wasu mutum-mutumi da ke da nasaba da addinin Confucian da na Taoism dai dai, sa'an nan kuma an sassaka mutum-mutumin da ke da nasaba da wadannan addinai 3 tare. Ban da wannan kuma, an sami mutum-mutumin sassaka game da mutanen tarihi a nan.

Halayyan musamman da mutum-mutumin sasakan Dazu ke da su su ne dimbin mutum-mutumi da nagartacciyar fasahar sassaka da abubuwan da mutum-mutumin suka shafa da kuma hali mai kyau da suke ciki.(Tasallah)