Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-03 16:54:23    
Shan lemo kadan zai ba da taimako ga rage kiba

cri

Wani sabon nazari da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka yi ya tabbatar da cewa, idan an sha lemo da yawa, to zai kara kiba. Ban da wannan kuma masu ilmin kimiyya sun gano cewa, idan samari masu kiba sun sha lemo kadan, to zai ba da taimako gare su wajen rage kiba.

Bisa labarin da muka samu daga jaridar likita ta kasar Jamus, an ce, masu ilmin kimiyya na asibitin yara na Boston na kasar Amurka sun yi wani bincike kan samari 103 da shekarunsu ya kai 13 zuwa 18 da haihuwa. Kusan rabin da ke cikinsu ba su sha lemo da Coca Cola da kuma abin sha da ke hade da sukari ba a cikin rabin shekara.

A karshe dai, sakamakon nazarin ya bayyana cewa, wadanda suka tsaya tsayin daka kan kin shan lemo, nauyinsu ya ragu. Daga baya kuma masu ilmin kimiyya sun gano cewa, idan wani mutum ya sha lemo mai zaki da yawansa ya kai millilitre 330 a ko wace rana, to nauyinsa zai karu da kilogram daya a cikin wata guda.

Yanzu bari mu gabatar muku wata shawara daban game da tabaraun kare rana.

Hasken rana na kasar Nijeriya yana da karfi sosai, shi ya sa sanya tabaran kare rana zai bayar da taimako wajen kare idanu. Amma wata kwararriya ta kasar Amurka a kan ilmin idanu ta bayyana cewa, ya fi kyau a zabi tabaraun kare rana da ke da gilashi mai launin rawaya a maimakon launin shudi domin gudun cututtukan idanu.

Bisa labarin da muka samu daga kamfanin dillancin labaru na Reuters, an ce, wata furfesa a fannin ilmin idanu ta jami'ar Columbia ta Amurka ta gano cewa, haske mai launin shudi da ke cikin hasken rana yana yin mumunar illa ga idanun mutane, kuma wannan muhimmin dalili ne da ya sa tsofaffi suke zama makafi. Sabo da haka ta bayyana cewa, gilishi mai launin rawaya yana iya tace haske mai shudi, ta haka za a rage yawan haske mai shudi da ke shiga idanu, amma gilishi mai launin shudi zai zabi hashe mai shudi. Shi ya sa ta ba da shawarar cewa, ko samari ko tsofaffi, bai kamata a sa tabaran kare rana da ke da gilishi mai launin shudi ba.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan kundin sani na yara na farko da kasar Sin ta buga.(Kande)