Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-02 15:33:51    
Bayani game da kabilar Ozbek

cri

Da farko dai za mu bayyana muku wata karamar kabilar kasar Sin, wato kabikar Ozbek. Sannan kuma za mu karanta muku wani bayani kan yadda wani dan kabilar Ozbek yake yin harkokin agaji. Yanzu ga bayani game da kabilar Ozbek.

Yawancin mutanen kabilar Ozbek suna da zama a birnin Yining da garin Tacheng da yankin Kashi da birnin Urumqi da yankin Shache da Yecheng na jihar Xinjiang ta kabilar Ugyur mai cin gabashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Ozbek ya kai dubu 12 da dari 3 da saba'in. Suna da yaren Ozbek da yaren Uygur.

A cikin farkon rabin karni na 14 da ya gabata, mutanen Ozbek sun yi zama a karkashin mulkin kasar Qinchar, sun bi addinin Musulunci. Sannan kuma an kafa wata karamar kasa ta Ozbek wadda take karkashin kasar Qinchar. Daga baya, kasar Qinchar ta mutu, an fara kiran mutanen Ozbek cewar mutanen kabilar Ozbek.

Domin mutanen kabilar Ozbek suna zama a yankunan da hanyar siliki take ratsawa, kafin tsakiyar karnin 19 da ya gabata, yawancin mutanen kabilar Ozbek sun yi kasuwanci. Da farko dai, sun kafa kungiyoyin safari, kuma sun dilla kayayyaki iri iri a tsakanin jiyar Xinjiang da sauran yankunan tsakiyar nahiyar Asiya. Sannan, sun fara bude kantunan sayar da kayayyakin masarufi. Wasu kuma sun yi sana'ar kiwo da ta aikin gona.

Domin yawancin mutanen kabilar Ozbek suna zama a birane da garuruwa, sun rinjaye sauran kananan kabilun kasar Sin wajen samun ilmi. Kabilar Ozbek tana da kwararru da malamai da yawa. Halin tattalin arziki da na al'adu da mutanen kabilar Ozbek suke ciki suna matsayi mai kyau. Zaman rayuwar jama'ar Ozbek ma yana da kyau.

Bugu da kari kuma, adabin kabilar Ozbek ciki har da rubutattun wakoki na tarihi da dogon wakoki na tatsuniyoyi da wakokin jama'a da karin maganganu da kacici-kacici da dai sauransu suna da launi iri iri.

A waje daya kuma, kide-kiden jama'ar kabilar Ozbek suna da dadin ji, kuma ana wasan su cikin sauri.

A wani gidan kabilar Ozbek, yawancin iyaye da 'ya'yansu su kan zama ba a wuri daya ba, amma a cikin wasu gida, iyalan zuriyoyi 3 suna zama tare. Mutanen kabilar Ozbek suna da al'adar yin aure da kabilar Uygur da kabilar Tatar. Iyaye ne suke kulawa da auren 'ya'yansu. Iyayen amariya suna neman kyauta daga iyalan ango. A cikin wani gida, idan wa bai yi aure ba, kane bai iya yin aure ba. Kuma ba a yarda da a yi aure da wani mutumin maras bin addinin Musulunci ba. Bisa al'adar kabilar Ozbek, a kan shirya bikin aure da maraice a gidan amariya. Imam ne yake shugabantar bikin aure.

Gidajen mutanen kabilar Ozbek suna da salo-salo. Kamar yadda dukkan mutane masu bin addinin Musulunci suke yi, mutanen kabilar Ozbek suna da sha'awar cin naman shanu da tumaki da naman doki. Kuma su fi son shan nonon shanu. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Ozbek suna kuma taya murnar bukukuwa na "Babbar Sallah" da "Karamar Sallah".(Sanusi Chen)