Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-02 15:31:18    
Talebijin na zamani ya kyautata zamantakewar fararren hula na kasar Sin

cri

Talebijin na zamani shi ne talebijin da ke yi amfani da fasahar zamani yayin da ake yin shirye-shiryen talebijin. Shirye-shiryen talebijin na zamani suna da halayen musamman masu kyau idan an kwakwata su da na talebijin iri na tsohon yayi. Alal misali, muryar shirye-shiryen talebijin na zamani tana da kyau, shirye-shiryen suna da matukar yawa, kuma shirye-shiryen suna da karfin kawar da daukewar hoto. Ban da wannan kuma, masu yin amfani da talebijin na zamani suna iya zabi shirye-shiryen talebijin da ke so. Haka kuma abin da ya fi jawo hankulan mutane shi ne talebijin na zamani yana iya amfanin na'urar kwamfuta, ana iya more zaman rayuwa ta yin amfani da shi.

Wang Qinpu, wani tsoho ne da ke da zama a birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin, yanzu shekarunsa ya kai 77 da haihuwa. Talebijin da ke gidansa ya zama kamar wani abokin arziki rayuwa shi da matarsa. Yau shekara guda da ta gabata, talebijin na zamani ya zama wani bangare na zaman rayuwarsu. Wang Qinpu ya gaya wa wakilinmu, cewa ba kawai suna iya kallon shirye-shiryen talebijin masu yawa ta talebijin na zamanni ba, har ma abin da ya fi ba shi mamaki shi ne, ya iya sayen littattafan da yake so ta talebijin.

"Na iya ganin littattafai masu amfani sosai da ake nunawa a ko wane mako a talebijin na zamani, idan na ga littattafan da nake so, sai na saye su ta talebijin na zamani, ta haka ya saukaka mani sosai a fannin sayen littattafai."

Bisa shirin raya talebijin na zamani da gwmnatin kasar Sin ta tsara, kasar Sin za ta daina yin amfani da talebijin iri na tsohon yayi a shekara ta 2015, da kuma fara yin amfani da talebijin na zamani a duk fadin kasar. Mataimakin shugaban sashen kimiyya da fasaha na babbar hukumar kula da harkokin talebijin da fina finai da rediyo ta kasar Sin Wang Lian ya bayyana cewa

"za mu aiwatar da shirinmu na raya talebijin na zamani bisa matakai hudu a yankin gabashin kasar Sin da na tsakiyar kasar da kuma na yammacin kasar. Kuma ya zuwa shekara ta 2015, za mu yi kokarin daina yin amfani da talebijin iri na tsohon yayi da kuma fara yin amfani da talebijin na zamani."

Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suke yin amfani da talebijin na zamani na kasar Sin ya zarce miliyan hudu. Ba kawai suna iya kallon shirye-shiryen talebiji masu kyau kwarai da gaske ba, har ma suna iya samun labarai kan al'adu da ba da ilmi da zirga-zirga.

Ta wadannan ayyukan hidima, talebijin na zamani ya kawo sauki sosai ga mutanen da ke da aikin yi wadanda su kan tashi daga gida da safe da kuma koma gida da dare. Chen Hong da matarsa da suke da zama a birnin Hangzhou suna da wani yaro mai shekaru kadan, kullum su kan sha aiki sosai. Chen Hong ya bayyana cewa, bayan da suka fara yin amfani da talebijin na zamani, sun daina bata lokaci sosai domin zuwa cetane da sauran kayayyakin masarufi.

"Alal misali, na zabi shinkafa da nake so in saya ta talebijin, daga baya kuma na zabi yawan shinkafa da nake so, bayan haka kuma na tabbatar da abin da na zabi ta hanyar latsa maballin da ke kan macanjin tasoshin talebijin, ta haka na kan sayi shinkafa ta talebijin na zamani."

Game da Madam Chu Mei, yanzu ta riga ta saba da yin amfani da talebijin na zamani. A ko wace rana da safe, ta samu labarin zafin yanayi wajen motsa jiki ta talebijin na zamani, ban da wannan kuma ta iya zabar wasannin kwaikwayo na talebijin da take son kallo. Amma abin da ta fi nuna gamsuwa shi ne, tana iya ganin sharhin da malamai suka yi game da yaronta da kuma makin da yaronta ya samu kan karatu, a waje daya kuma yaronta ya karu sosai ta kallon laccocin da shahararrun malamai suka bayar ta talebijin na zamani.

"sabo da dukkan 'yan makarantun firamare suna son jin darussan da shahararrun malamai ke bayarwa da kuma samun ilmin daga bakin shahararrun malamai, amma ba safai a kan samu irin wannan zarafi ba. Yanzu yara suna iya more irin wannan nagartaccen ilmi ta talebijin na zamani, a ganina, wannan zai ba su alheri sosai."

Bisa labarin da muka samu daga babbar hukumar kula da harkokin talebijin da finafinai da kuma rediyo ta kasar Sin, an ce, tashi a hankali, ana raya ayyukan yin amfani da talebijin na zamani a yankunan da ke tsakiya da yammacin kasar Sin da kuma yankuna marasa ci gaba na kasar Sin. A nan gaba, fararren hula na kasar Sin mafi yawa za su iya kallon talebijin na zamani, ban da wannan kuma za su mayar da talebijin na zamani a matsayin mai ba da taimako ga zamansu.(Kande Gao)