A ran 28 ga wata, a yayin da ministan yada labarai da ilmi na kasar Togo yake amsa tambayoyin da wakilin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya yi masa, ya yi babban yabo ga hadin kai da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi, ya ce haka, 'muna yabawa kasar Sin, musamman hadin kai da take yi da kasar Togo. Bangarorin biyu sun fara wannan hadin kai ne tun daga shekaru da yawa da suka wuce.'
Minista ya ce, 'tun can shekaru aru aru ya kasance akwai dangantakar abuta da hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Tushen hadin kansu shi ne yin zaman daidai wa daida da amincewar juna. Ziyarar da firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya kai a Afirka ta kara karfafa irin wannan dangantakar hadin kai. Dangantakarsu ta zama wani abin koyi ga hadin kai tsakanin kudu masu kudanci.
Minista ya ci gaba da cewa, idan ake kwatanta kasar Sin da kasashen Afirka, ana iya ganin cewa, kasar Sin ta fi samun saurin bunkasuwa, ko da yake haka ne, amma kasar Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, kuma ba ta sanya ko wane salon siyasa a kan kasashen Afirka da karfi ba. A matsayi daya na kasashe masu tasowa, kasar Sin tana son ba da taimako da hada kai da kasashen Afirka domin samun bunkasuwar Afirka.
Da aka tabo magana a kan taron koli na dandalin tattauna a tsakanin Sin da Afirka da za a shirya a birnin Beijing, minista ya ce, shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe zai halarci taron tare da sauran shugabanni da manyan jami'an kasashen Afirka. Kasar Togo tana fatan alheri sosai ga wannan taro, tana fata za a iya kara kyautata dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka a gun wannan taro.(Danladi)
|