Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-29 14:43:14    
Bankin tsakiya na kasar Sin ya sake kara yawan ruwan kudi

cri

A kwanakin baya ba da dadewa ba, bankin jama'ar kasar Sin wato bankin tsakiya na kasar ya sake kara kashi 0.27 cikin dari na ruwan kudin Sin na Renminbi da ake ajiyewa a bankunan kasar. Wannan ne karo na biyu da bankin tsakiya na kasar Sin ya kara yawan ruwan kudin da ake ajiyewa a bankunan kasar. Babban makasudin yin haka shi ne, domin sassauta saurin karuwar kudin jari mai yawa da ake zubawa da kuma rancen kudi mai yawa da ake bayarwa a kasar.

Tun farkon shekarar nan, ana ta bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin da sauri sosai. Manyan dalilai biyu da suka sa haka, su ne kudin jari da ake zubawa kan kadarori kamar gidaje da gine-gine da makamantansu da kayayyaki da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Alal misali, yawan kudin jari da aka zuba kan kadarori kamar gidaje da gine-gine da makamantansu ya karu da kimanin kashi 30 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, haka nan kuma a cikin farkon rabin shekarar nan, yawan rancen kudi da bankuna daban daban suka bayar, ya riga ya dauki kashi 90 cikin dari bisa jimlar rancen kudi da suke shirin bayarwa a duk shekara. Ta haka an kara gamuwa da matsaloli wajen gudanar da tsarin tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata, musamman ma a fannin makamashi da albarkatun kasa.

Da Malam Xia Bin, masanin ilmin kudi da ke aiki a cibiyar nazarin harkokin raya kasa ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya tabo magana a kan sake kara yawan ruwan kudi da ake ajiyewa a bankunan kasar, sai ya bayyana cewa, "babban makasudin kara yawan ruwan kudi da ake ajiyewa a bankunan kasar shi ne domin kyautata halin da ake ciki yanzu a kasar dangane da tattalin arziki daga manyan fannoni, wato yawan kudin musanya da kasar ta tanada da kuma yawan kudi da ta samar sun karu da sauri. An dauki wannan matakai ne domin ba da tabbaci ga bunkasa tattalin arziki da sauri yadda ya kamata. Don rage yawan rancen kudi na dogon lokaci da aka bayar ya karu da sauri da bai kamata ba, an kara ruwan rancen kudin mai yawa."

Malam Xia Bin ya kara da cewa, bayan da aka kara ruwan rancen kudi da bankunan kasar ke bayarwa, yawan kudi da masana'antu ke kashewa wajen samar da kayayyaki ma zai karu. Ta haka masana'antu ba za su kara nuna zafin nama wajen zuba jari a wasu fannoni ba. Kana saurin karuwar rancen kudi da ake bayarwa ma zai sassauta.

Dangane da tasiri da matakin nan ya haddasa ga jama'a, Malam Li Lei wanda ke aiki a kafofin watsa labaru na birnin Beijing ya bayyana cewa, "a ganina, babu babban tasiri da matakin nan ya haddasa ga jama'a. Alal misali, da ma yawan kudi da nake biyawa a ko wane wata domin mayar da rancen kudi da na ci daga wajen banki kadan ne. Sabo da haka kara ruwan rancen kudi da bankuna ke bayarwa ba wani abu ba ne gare ni."

Mataki da bankin tsakiya na kasar Sin ya dauka wajen kara ruwan kudin ajiyewa da na rancen kudi da bankunanta ke bayarwa ya jawo hankulan gamayayar kasa da kasa. Wasu kwararru suna ganin cewa, nan gaba ba sau daya ba ba sau biyu ba, bankin tsakiya na kasar Sin zai ci gaba da kara ruwan kudin nan kadan. Malam Xia Bin ya bayyana a kan wannan cewa, "al'amarin ya danganci sakamako da za a samu wajen kyautata harkokin tattalin arzikin kasa daga manyan fannoni. A lokacin da ake yin haka, mai yiwuwa ne za a kara daga yawan kudi da bankuna ke bayarwa ga bankin tsakiya bisa jimlar kudin ajiya da suke samu daga wajen jama'a. Sa'an nan za a dauki sauran matakai da dama wajen sanya ido ga sabbin ayyuka da ake yi a fannin kare muhalli da albakartu da sauransu. Idan an sami sakamako mai kyau, to, bankin tsakiya na kasar Sin ba zai kara daukar matakai wajen kara ruwan kudi da ake ajiyewa a bankunan kasar ba. " (Halilu)