Kuna sane da cewa, alamun nuna manufar hanyoyin mota dake kusa da filin gasa suna da muhimmanci sosai ga aikin gudanar da wata gagarumar gasa. An kafa alamun nuna manufar hanyoyin mota da yawa a kan hanyar zuwa filin gasa ta wasan softball kuma direbobin motocin musamman na gasar din sun gane su sosai, amma duk da haka, ' yan kallo da yawa sun yi koke-koken cewa ba su samu saukin ganewa ba, kuma ba su samu saukin daukar mota domin koma gida ba bayan an gama gasa da aka yi a dare.
Game da wannan magana dai, Mr. yang Shuan ya tabbatar da, cewa ko shakka babu za a kara kyautata halin zirga-zirga a nan Beijing lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 domin an kadddamar da wani shirin muhimman tsare-tsare na yin hidima ga harkokin zirga-zirga a Beijing, wato ke nan za a kafa hanyoyin musamman domin taron wasannin Olympic, wadanda ba za su kawo cikas ga zaman yau da kullum na mazauna birnin ba.
A takaice dai, ayyukan shirye-shirye na gasar cin kofin duniya ta wasan softball da aka yi a wannan gami sun gamsar da hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa da kuma karamar kungiyar sa ido ta kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Shugaban hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa Mr. Don Porter ya fadi, cewa mun yi farin ciki matuka da kai ziyarar gani da ido a ayyukan gini na filaye da dakunan wasa, wadanda suka dace da bukatunmu sosai.( Sani Wang ) 1 2 3
|