Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-28 15:29:09    
Bayyanin kan wasannin kwaikwayo na kasar Sin

cri

A nan kasar Sin akwai wasannin kwaikwayo fiye da goma ciki har da wasan Beijing Opera da wasan kwaikwayon Yu wato Henan da wasan kwaikwayon Huangmei da na Kunshan. Da farko dai bari mu yi 'dan bayani kan wasan kwaikwayon Beijing wato Beijing Opera .

A cikin wasan Beijing Opera na kasar Sin akwai manyan 'yan wasa guda 4 . Su ne mai gida da uwar gida ko yarinya da 'dan fuska mai furani (flowery face) da kuma 'dan kama mai ban dariya.

Mai gida yana nufin wani namiji wanda yake da shekaru 30 zuwa 50. A galibin lokaci ya zama babban mutum ko sarki ko janar ko minista .

Uwar gida tana nufin wata mace wadda take da shekaru 30 zuwa 50 . A galibin lokaci ta zama matar babban jami'i. Yarinya akwai iri biyu . Ta farko yarinya tana dauke da makamai kuma ta iya wasan sanda ko wuka . Ta biyu budurwa ce . A galibin lokaci ta zama yarinyar gida ko mai yin aikin hidima ga matar babban jami'i.

'Dan fuska mai furani yana nufin mutum wanda aka shafa launuka daban daban a kan fuskarsa. A galibin lokaci ya zama namiji mai kirki ko wanda yake da halin musamman.

'Dan kama mai ban dariya yana rayuwa a cikin rukuni maras karfi . Galibinsu suna da wayo ko abin da suka yi mai ban dariya ne.

Wasan kwaikwayo na Beijing wato Beijing Opera na kasar Sin a kan kira cewa , shi ne wasan kwaikwayo na wake-wake na gabas . Dalilin da ya sa ya sami wannan suna shi ne saboda ya tattara abubuwa masu kyau na wasannin kwaikwayo daban daban, kuma an haifar da shi a nan birnin Beijing.

Wasan kwaikwayon Beijing yana da tarihin shekaru fiye da 200 . Mafarinsa shi ne tsohon wasan kwaikwayo na Anhui dake kudancin kasar Sin . A shekarar 1790 , kungiyar wasan kwaikwayon Anhui ta farko ta shiga Beijing don halartar nune-nunen ranar haihuwar Sarki . Bayan haka kungiyoyin wasan kwaikwayon Anhui sun zo nune-nune a birnin Beijing bi da bi . A karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20 , bayan da aka tattara abubuwa masu kyau cikin shekaru masu yawa , sai aka haifar da wasan operar Beijing.

Wasan operar Beijing yana da shirye-shirye masu yawa. Kwararrun mutanen wasan kwaikwayon Beijing suna da yawa . Kungiyoyin nune-nunen wasan kuma suna da yawa

Yawan 'yan kallon wasan operar Beijing da tasirin da ya kawo ya kai matsayi na farko a nan kasar Sin a cikin dukannin wasannin kwaikwayo .

Mei Lanfang shi ne daya daga cikin 'yan fasahar wasan operar Beijing wadanda suka fi suna a duniya . An haife shi a shekarar 1894. Lokacin da ya cika shekaru 8 da haihuwa, ya fara koyon rera wasan operar Beijing .A shekarar 1905 wato lokacin da yake da shekaru 11 da haihuwa , sai ya hau dakali don nuna fasaharsa . A cikin rayuwarsa mai tsawon shekaru fiye da 50 , Mr. Mei ya haifar da halin musamman na fasaharsa . Shi namiji ne , amma a cikin shekaru 50 da suka wuce , kullum ya yi wasan da kayan Uwar gida ko yarinya. A shekarar 1919 Mei Lanfang ya jagoranci kungiyar wasan operar Beijing zuwa kasar Japan . Wannan karo na farko ne da aka nuna fasahar wasan operar Beijing a kasar waje . A shekarar 1930 , Mr. Mei ya jagoranci kungiyar zuwa kasar Amurka don nune-nune da ziyarce-ziyarce , kuma ya sami babbar nasara . A shekarar 1934 , bisa gayyatar da aka yi masa , ya kai ziyara a Turai kuma ya sami yabo da maraba kwarai da gaske daga rukunin wasan kwaikwayo na kasashen Turai.

Jama'a masu sauraro , abin da kuka saurara dazu nan shi ne bayanin kan wasan kwaikwayon Beijing . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan wasannin kwaikwayon Yu wato Henan .

Jama'a masu sauraro , yanzu sai ku 'dan shakata kadan, daga basani kuma za mu dawo domin karanta shirinmu na Me ka sani game da kasar Sin .

A cikin dogon lokacin tarihi , wasan kwaikwayon Yu wato Henan ya taba samun sunan babbar muryar Henan. A lokacin da, sabo da an yi wasan a kan dakalin da ake shiryawa a gindin Tudu , shi ya sa a kan kira shi da cewar , wasan operan tudu . Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin an fara yin amfani da Wasan kwaikwayon Henan . Wannan wasan yana yaduwa a lardin Henan da lardin Shandong da lardin Shanxi da lardin Hubei da Jihar Ningxia da Jihar Xinjiang da Lardin Qinghai da sauran larduna da jihohi bakwai . Wannan wasan daya ne daga cikin wasannin kwakwayo mafiya kasancewa da tasiri mai kyau . Wasan kwaikwayon Henan an haifar da shi ne a karshen Daular Ming zuwa farkon Daular Chin . A farkon lokaci an mai da hankali kan rera opera da murya kawai , shi ya sa ya sami kaunar jama'a farar hula . Saboda haka ya sami yalwatuwa da saurin gaske .Bayan da aka haifar da wasan kwaikwayon Henan , an sami rukunoni masu bambanci guda 4. Rukuni na farko shi ne muryar Xiangfu dake birnin Kaifeng . Rukuni na biyu shi ne muryar Donglu dake birnin Shangqiu. Rukuni na uku shi ne muryar Xifu dake birnin Luoyang . Rukuni na hudu shi ne Muryar Shahe dake birnin Luohe . Lokacin da ake yin wasan kwaikwayon Henan a kan yi amfani da wasu kayayyakin kide-kide . A cikinsu akwai sarewa da goge tamkar molo da pipa da kakakin sona da sauransu . Wasan kwaikwayon Henan yana da halin musamman sosai na Henan , kuma yana bayyana zaman yau da kullum na jama'a farar hula . Kafin shekarar 1927 a cikin wasan kwaikwayon Henan babu 'yan wasa mata . Bayan da aka bullo da 'yan wasa mata , sai wasu kwararrun 'yan wasa sun yi suna a dakalin wasan . Kamar su Chang Xiangyu da Chen Suzhen da Ma Jinfeng da Yan Lipin da Cui Lantian sun kafa rukuni na kansu daban daban.

Yawan shirye-shiryen gargajiyar Henan opera ya kai fiye da dubu . Galibin shirye-shiryen sun zo daga kagaggun labaran tarihi. Wasu kuma sun bayyana labarun aure da soyayya da kamilanci ko da'a . Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin , an yi nune-nunen wasannin kwaikwayo na zamani da sababin

shirye-shirye wadanda suka bayyana sababin labarun tarihi. Wannan ya sa aikin wasan kwaikwayon Henan ya sami sabon ci gaba .

Yau ko da ya ke wasan kwaikwayon Henan har ila yau ya sami kauna daga jama'a masu yawa , amma yalwatuwarsa tana kasancewa da wasu maganganu masu tsanani .

Jama'a masu saurare , a cikin shirinmu na yau mun yi 'dan bayani kan wasan Beijing Opera da wasan kwaikwayon Yu wato Henan . A cikin shirinmu na mako mai zuwa , za mu ci gaba da karanta bayani kan wasan kwaikwayon Huangmei da Wasan kwaikwayon Kunshan.  (Ado)