Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-27 19:26:34    
Labarin kasa na kasar Sin

cri

Kwanan baya, mun sami tambayoyi da yawa daga masu sauraronmu dangane da labarin kasa na kasar Sin. Kamar misali, a cikin wasikar da malam Baba Zubair daga birnin Zaria na jihar Kaduna ta kasar Nijeriya ya turo mana, ya tambaye mu, wane tsauni ne ya fi girma a kasar Sin? kuma wane tsauni ne ya fi tsawo a kasar Sin. Akwai kuma malama Hadiza Amin B wadda ita ma ta fito ne daga birnin Zaria ta ce, ina son in ji tarihin tsohon kogin nan mai dadadden tarihi, wato River Yangtse. Bayan haka, Zulai Malami, wata mazauniya daban ta birnin, ta rubuto mana cewa, wane irin tsiro ne kasar Sin ta fi nomawa? To, masu sauraro, bari mu amsa tambayoyin wadannan masu sauraro, mu bayyana muku kyawawan tsaunuka da koguna na kasar Sin.

Jamhuriyar jama'ar kasar Sin tana gabashin nahiyar Asiya da kuma yammacin gabar tekun Pasifik. Tana makwabtaka da kasar Koriya ta arewa a gabas, da Mongoliya a arewa, da Rasha a arewa maso gabas da kuma kasashen Kazakhstan da Kyrghizstan da Tadzhikistan a arewa maso yamma. Ban da wannan, kasar Sin tana kuma iyaka da kasashen Afghanistan da Pakistan da Indiya da Nepal da Bhutan a yamma da kuma kudu maso yammacinta. A kudu kuma, kasar Sin tana makwabtaka da kasashen Myanmar da Laos da Vietnam. Bayan haka, kusa kusa ne gabashin kasar Sin da kudu maso gabashinta suke da kasashen Koriya ta kudu da Japan da Phillippines da Brune da Malaysia da kuma Indonesia, duk da kasancewar teku a tsakaninsu. Fadin kasar Sin ya kai muraba'in kilomita miliyan 9 da dubu 600, wanda ya zo na uku a duniya, bayan kasashen Rasha da Canada.

Ya kasance da kyawawan duwatsu masu girma da yawa a maka-makan filayen kasar Sin. Daga cikinsu, akwai wani da ya fi shahara, wato dutsen nan mai suna Chomolangma. Dutsen Chomolangma yana Platon Qinghai-Tibet, wanda ake kiransa 'kololuwar tsaunuka a duniya', kuma yana kan iyakar da ke tsakanin Sin da Nepal, shi babban dutse ne daga cikin jerin tsaunuka na Himalaya, tsayinsa ya kai mita 8844.43, shi duste ne mafi tsayi a duniya.

Ban da wannan, a yammacin kasar Sin, ya kuma kasance da wani babban dutse wanda ake kira Kunlun. Tsawon dutsen Kunlun ya kai kilomita fiye da 2,500, shi dutse ne da ya fi tsawo a kasar Sin da kuma a nahiyar Asiya gaba daya, har ma ake yi masa kirari cewa, 'dutse ne na duwatsu'.

Kasar Sin ita ma daya daga cikin kasashen da suka fi samun koguna. A kasar, yawan kogunan da fadinsu ya wuce muraba'in kilomita 1,000 ya kai sama da 1,500. Kogin Yangtse kogi ne da ya fi girma a nan kasar Sin, haka kuma kogi mafi tsawo ne a nahiyar Asiya. Kogin ya taso ne daga dutsen Tanggula da ke Platon Qinghai-Tibet, sa'an nan ya doshi gabas, ya ratsa larduna da jihohi da birane da yawansu ya kai 11, daga karshe ya kwarara cikin tekun gabas. Tsawon kogin Yangtse ya kai kilomita 6,300 gaba daya, wato ke nan ya zama babban kogi na uku a duniya, wato bayan kogin Nile a Afirka da kogin Amazon da ke Latin Amurka. Ban da wannan, rawayen kogi wanda tsawonsa ya kai kilomita 5,500, ya kasance babban kogi na biyu a kasar Sin. Kogin ya sami asalinsa ne a dutsen Bayankala da ke tsakiyar lardin Qinghai, kuma ya ketare larduna da jihohi 9, kuma yana malala zuwa tekun Bo daga karshe.

Kasar Sin tana kuma da maka-makan filayen gonaki masu albarka, inda ake iya noman abinci iri daban daban. Fadin gonakin da kasar Sin take da su a halin yanzu ya kai kadada miliyan 130 da dubu 40, kuma sararin kasa da ke a arewa maso gabashin kasar Sin da arewacinta da kuma gabobin kogin Yangtse da kuma Pearl Delta da kwarin Sichuan su ne muhimman shiyyoyin da aka fi samun gonaki. Sararin kasa da ke arewa maso gabashin kasar Sin wanda ke da fadin muraba'in kilomita dubu 350 sararin kasa ne da ya fi fadi a kasar Sin, kuma filayen kasa a nan baki ne kiris, inda ake noman alkama da masara da wake da dawa da dai sauransu. A sararin kasa da ke arewacin kasar Sin kuma, ake yawan noman alkama da masara da shimkafa da dai sauransu. Kana kuma a sararin kasa da ke kogin Yangtse, sabo da kasancewar koguna da tabkoki masu yawa a nan wurin, shi ya sa ake yawan samun shimkafa da kifaye a shiyyar, har ma aka ba ta suna 'garin shimkafa da kifaye'. (Lubabatu)