Daga karshen karni na 16 zuwa farkon karni na 17, 'yan mishan na kasashen yamma sun sauko nan kasar Sin daya bayan daya, kuma sun huduba tare da gabatar da wasu sakamakon da aka samu wajen yin bincike kan kimiyyar halittu na zamanin yau. Masanin kasar Sin Xu Guangqi da wadannan 'yan mishan sun yi hadin huiwa wajen gabatar wa rukunonin masu fasahohi na kasar Sin kimiyyar zamani na kasashen Yamma cikin himma da kwazo, shi ya sa Mr Xu Guangqi ya zama mashahurin dan kimiyya na kasar Sin na wancan zamani.
An haifi Xu Guangqi a shekarar 1562 a birnin Shanghai na kasar Sin. Kamar yadda sauran duban 'yan boko suka yi, burin Xu Guangqi shi ne don neman samun wani mukamin gwamnati a hedkwatar kasar Sin, amma ya fi sauran masu fasahohi fiffiko bisa sanadiyar ganawar da ya yi da dan mishan kasashen Turai mai suna Matteo Ricci, a karshe dai ya zama mashahurin dan kimiyya.
Wajen shekarar 1600, Mr Xu Guangqi ya tashi daga birnin Shanghai zuwa birnin Beijing don neman samun mukami ta hanyar jarrabawar da aka yi, lokacin ya yada zango a birnin Nanjing na kasar Sin, sai ya ji an ce da akwai wani dan mishan mai suna Matteo Ricci a can, shi Matteo Ricci ya kan gabatar da wasu ilmin kimiyya na kasashen yamma. Wasu 'yan boko na birnin Nanjing suna son yin cudanya da dan mishan nan. Ta hanyar gabatarwa da sauran mutane suka yi ne, Mr Xu Guangqi ya gana da Mr Matteo Ricci, abubuwan da ya ji daga wajen Matteo Ricci abubuwa ne da bai taba samuwa ba a da daga wajen littattafan da ya karanta. To daga nan ne, yana da sha'awa sosai a kan kimiyyar kasashen yamma, sa'anan kuma ya zama wani mabiyin addinin Catholicism.
Bayan wasu shekaru da suka wuce, Xu Guagqi ya sami wani mukami a birnin Beijing. Ta hanyar yin cudanya da Matteo Ricci da sauran 'ya mishan na kasashen yamma, sai ya ji cewa, koyon ilmin kimiyya na kasashen yamma na da amfani ga kara wadatar da kasar mahaifarsa, saboda haka ya yi niyyar maido da Matteo Ricci don ya zama malminsa wajen koyon ilmin yanayin sararin samaniya da ilmin lissafi da ilmin safiyo da dabarun kera makamai da sauran ilmin kimiyya, daga nan sai ya kulla huldar abokantaka da Matteo Ricci har cikin shekaru masu yawa.
Taimakon da Xu Guangqi ya yi ga raya kimiyyar kasar Sin a wancan zamani ya bayyana wajen fassara da gabatar da littattafan kasashen yamma. Cikin hadin guiwarsa da Matteo Ricci ne Xu Guangqi ya fassara wani shahararren littafin lissafi dangane da ilmin Geometry, ya yi aikin cikin shekara daya ko fiye, ya yi gyare-gyare sau da yawa, sa'anan kuma ya buga littafin nan a kasar Sin, wannan ya zama littafin lissafi da aka fassara a karo na farko a tarihin kasar Sin. Sa'anan kuma ya yi hadin guwia da Matteo Ricci ya fassara wasu shahararrun littattafan kimiyya dangane da aikin safiyo da ayyukan ruwa da dai sauransu. Xu Guanqi ya kuma wallafa littattafan kimiyya da yawa dangane da yanayin kasa da ilmin sararin samaniya da abubuwan tarihi.
Wata gudumuwa daban da Xu Guangqi ya ba da ga raya fasahohin kimiyya ita ce, ya wallafa wani littafi dangane da harkokin noma. Littafin nan na da kalmomin da yawansu ya kai dubu 700, ya takaita fasahohin aikin noma na zamanin aru aru na kasar Sin, kuma ya tattara tsare-tsare da manufofin noma da kayayyakin noma da halayen musamman na amfanin gona da fasahohin noma da dai sauransu a cikin littafin, ya tanadi takardun abubuwan tarihi da yawa.
A duk rayuwar Xu Guangqi, ya wallafa littattafai da yawan irinsu ya kai 10 tare da kalmomin da yawansu ya kai miliyan 3, ya mika wa matalauta kudi da kayayyaki da sarki ya ba shi kyauta, ya yi kishin kimiyya, ya ba da gudumuwa mai muhimmanci ga lissafi da yanayin sararin samaniya da tsarin kalanda da aikin soja da noma da sauransu. Ya kafa tushen yin tunani da hasashe da fasahohi na kasar Sin wajen yin jurewa daga zamanin aru aru zuwa zamanin yau.(Halima)
|