Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-27 18:48:58    
Sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana buri ne iri daya na dukan Sinawa a duk duniya

cri

Yanzu an kafa kungiyoyin jama'a da ke goyon bayan dinkuwar kasar Sin a kasashe da yankuna fiye da 80 a duk duniya. Wadannan kungiyoyi suna yin kokari cikin himma da kwazo wajen kiyaye kwanciyar hankali tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da kuma raya huldar da ke tsakanin gabobin 2 bisa manufar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Tun daga ran 26 zuwa ran 27 ga wannan wata, shugabannin kungiyoyin sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin da jami'an kungiyoyin da abin ya shafa fiye da 130 na kasashen waje da Hong Kong da Macao da kuma Taiwan sun zo nan babban yankin kasar Sin, sun yi mu'amala a fannonin ayyukansu da sakamako mai nagarta da suka samu, sun kuma yi bayani kan burinsu na kin amincewa da kawo baraka ga kasar Sin da neman 'yancin kan Taiwan, da kuma sa kaimi kan babban aikin dinkuwar kasar Sin cikin ruwan sanyi.

Wakar kungiyar sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana ta jama'ar Taiwan, wadda aka samar da ita bisa wata wakar gargajiya ta Taiwan, ta bayyana burin 'yan uwanmu na Taiwan, wato suna kishin samun dinkuwar mahaifa cikin lumana.

Shugaban kungiyar sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana ta birnin Washington na kasar Amurka Mr. Huang Qizhi ya yi shekaru fiye da 30 yana yin ayyuka da yawa wajen ingiza dinkuwar mahaifa cikin lumana. A shekaru 1980, ya rubuta bayani kan ra'ayinsa kan 'kasa daya amma tsarin mulki biyu'. Ya ce,'Jama'a suna bukatar gudanar da 'kasa daya amma tsarin mulki biyu', ma iya cewa, za a gudanar da 'kasa daya amma tsarin mulki biyu' ne domin moriyar jama'a. Watakila za a sami babban sabani a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Amma bangarorin 2 za su yi cudanya da mu'amala a tsakaninsu, ta haka za su kara fahimtar juna. Bayan da aka gudanar da 'kasa daya amma tsarin mulki biyu', kasar Sin za ta kara karfinta.'

Tun bayan da shekarar 2000 har zuwa yanzu, Sinawa 'yan kaka gida da 'yan uwa na gabobin 2 sun tafiyar da harkar kin amincewa da neman 'yancin kan Taiwan da kuma sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin a duk duniya. Har zuwa yanzu, an kafa kungiyoyin sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana ko kuma kungiyoyi kamar irinsu fiye da 170 a kasashe da yankuna fiye da 80 a duniya, wadanda suke ba da gudummuwa mai yakini wajen kare kwanciyar hankali tsaknain gabobin 2 da kuma raya huldar da ke tsakanin gabobin 2 bisa manufar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Mataimakin shugaban kungiyar sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana ta kasar Chile Mr. Wang Weijiang ya bayyana cewa, kungiyoyin sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin ruwan sanyi da ke kasashen waje suna tattara karfin kishin kasa na Sinawa 'yan kaka gida, suna yin amfani da fifikonsu su ba da gudummuwa wajen ingiza dinkuwar mahaifa cikin lumana. Ya ce,'Kungiyoyin sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana da ke kasashen waje suna tattara karfin kishin kasa na 'yan kabilar Sin da ke kasashen waje, suna neman kin amicewa da neman 'yancin kan Taiwan da ingiza dinkuwar kasar da kuma bauta wa moriyar kasa da ta kabilar Sin. Kungiyoyin sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana sun tattara karfin rukunnoni masu sada zumunta da kasar Sin da karfin Sinawa 'yan kaka gida da karfin 'yan uwanmu na Taiwan da kuma karfin mahaifa.'

Tun bayan da shekarar 2000 har zuwa yanzu, Sinawa 'yan kaka gida sun yi babban taron sa kaimi kan dinkuwar kasar Sin cikin lumana a biranen Berlin da Washington da Tokyo da Moscow da Vienna, sun yi kokari wajen yaki da yunkurin kawo baraka ga kasar Sin da masu neman 'yancin kain Taiwan suke yi. Za a yi a wannan muhimmin babban taro a yankin musamman na Macao na kasar Sin tun daga ran 13 zuwa ran 16 ga watan Disamba na wannan shekara, inda za a gayyaci wakilan Sinawa 'yan kaka gida da kwararru na gabobin 2 da na Hong Kong da Macao da kuma shahararrun mutane na rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar da su tattauna kan ingiza yin mu'amala tsakanin gabobin 2 wajen tattalin arziki da ciniki da al'adu, da kuma raya huldar da ke tsakanin gabobin 2 bisa manufar zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Tasallah)