Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-27 08:58:49    
Kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin ta sami kyawawan fasahohi a gun gasar cin kofin duniya

cri

Daga ran 12 zuwa ran 23 ga watan Satumba,an yi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kwando ta mata ta 15 a jihar Sao Paulo ta kasar Brazil,kungiyar kasar Sin ba ta shiga jerin kungiyoyi guda takwas masu karfi ba,amma duk da haka `yan wasan kasar Sin sun sami kyawawan fasahohi a gun gasar,kuma suna so su cim ma sabon burinsu wato suna so su sami sakamako mai kyau a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekara ta 2008.

Gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kwando ta mata ita ce gasa ta matsayin koli a duniya,shi ya sa dukkan kungiyoyin duniya mafiya karfi sun shiga wannan gasa.Kuma kungiyar kasar Sin tana cikin karamin rukuni daya tare da kungiyar kasar Amurka da ta kasar Rasha da ta kasar Nijeriya.Kamar yadda kuka sani,kungiyar kasar Amurka ta taba zama zakarar gasar cin kofin duniya sau biyu,kungiyar kasar Rasha ita ma ta zama lambatu a duniya,ban da wannan kuma kungiyar kasar Nijeirya ita ce zakara ta Afirka.Halin da kungiyar kasar Sin ke ciki ya nuna mana cewa tana shan wahala.Makin gasa tsakaninta da ta kasar Amurka shi ne 72 bisa 119,da ta kasar Rasha shi ne 66 bisa 86,a gun gasar karamin rukuni ta karshe,ta lashe kungiyar kasar Nijeriya da 71 bisa 59,ta zama lambatiri a cikin wannan karamin rukuni kuma ta shiga jerin kungiyoyi guda 12 masu karfi na gasar.Daga baya,kodayake ta lashe kungiyar kasar Faransa,amma bisa ka`idar gasa da aka tanada,ba ta shiga jerin kungiyoyi guda takwas masu karfi ba,sai kungiyar kasar Faransa ta shiga.

Game da wannan,`yan wasan kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin sun bayyana cewa,a gun gasar da suka yi,sun tara fasahohi masu daraja,yanzu dai suna cike da imani.`Yar wasa ta tsakiya Chen Xiaoli tana ganin cewa,daga gasar tsakaninsu da kungiyar kasar Amurka da ta kasar Rasha da ta Czech,ta kara gane cewa ya kasance da rata tsakanin kungiyar kasar Sin da sauran kungiyoyin duniya masu karfi.Ta ce:`Alal misali,fasahar kama kwallo a karkashin kwando ta kungiyar kasar Sin ba ta da kyau,kuma karfinmu bai kai na kungiyoyin Amurka da Turai ba.`

A hakika dai,dalilin da ya sa kungiyar kasar Sin ba ta sami sakamakon da ta kima ba shi ne domin `yan takaran da ta gamu sun fi su karfi bisa babban mataki.Zaunannen mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Li Yuanwei ya bayyana cewa,ya gamsu da kokarin da `yan wasan kasar Sin suka yi.Ya ce:`Daga gasar da aka yi,ana iya ganin cewa,lalle kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin ta riga ta sami babban ci gaba,na hakake cewa kungiyar kasar Sin tana da makoma mai kyau.`

Babban malamin koyarwa na kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin `dan kasar Austrelia Tom Maher shi ma ya dauka cewa,kamata ya yi kungiyar kasar Sin ta yi alfahari saboda matsayinta ya dada daguwa a bayyane,kuma ta tattara fasahohi masu tsokana.

Ban da wannan kuma,daga gasar da aka yi,kungiyar kasar Sin ta tarar da wasu matsalolin fasaha,alal misali,`yan wasan kasar Sin ba su iya jefa kwallo cikin kwando da saurin gaske ba da dai sauransu.Kan wannan,zaunannen mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Li Yuanwei ya yi nuni da cewa,fasahar wasa ta `yan wasan kasar Sin ba ta da kyau sosai,amma ya yarda da ra`ayin da babban malamin koyarwa Maher ya nuna wato muhimmin burin shiga wannan gasar cin kofin duniya na kungiyar kasar Sin shi ne don tara fasahohi domin taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008.Ya ce: `A takaice dai,ana jin bakin ciki,amma mun riga mun sami sakamako masu daraja daga gasar,wato bayan gasar nan,matsayin gasa na kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin ya shiga wani sabon mataki.kuma matsakaicin shekarun `yan wasan kasar Sin da haihuwa ya kai 23 ne kawai,shi ya sa akwai izni da yawa a gabansu.`

Kafin taron wasannin Olimpic na Beijing,kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin za ta shiga wata babbar gasa daban wato taron wasannin Asiya da za a yi a Doha na kasar Quatar a karshen wannan shekara.Babban malamin koyarwa Maher yana fatan kungiyar wasan kwallon kwando ta mata ta kasar Sin za ta sami sakamako mai kyau saboda gasar nan ita ma tana da muhimmanci sosai. (Jamila Zhou)