Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-27 08:56:17    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(22/09-27/09)

cri

Ran 24 ga wata a birnin Beijing,kwamitin wasannin Olimpic na duniya da kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing sun daddale wata yarjejeniya game da batun kafa kungiyar dauka hoto ta duniya musamman domin taron wasannin Olimpic na Beijing tare da kamfanin dillancin labarai na Assosiated Press na kasar Amurka da kamfanin Reuter na kasar Ingila da kuma kamfanin AFP na kasar Faransa.Bisa yarjejeniyar da aka daddale,kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing zai samar da wajababbun sharuda a karkashin jagorancin kwamitin wasannin Olimpic na duniya ga `yan jaridun dauka hoto na wadannan kamfanoni uku,daga baya kuma kungiyar dauka hoto ta duniya za ta samar da kyawawan hotunan gasannin da za a yi domin yin farfaganda.

Ran 24 ga wata,a birnin Madrid na kasar Spain,an kammala gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon badminton ta shekara ta 2006,`yan wasa Fu Haifeng da Cai Yun daga kasar Sin sun zama zakaran gasa ta tsakanin maza biyu biyu,dan wasa Lin Dan daga kasar Sin ya zama zakaran gasar maza,`yar wasa Xie Xinfang daga kasar Sin ta zama zakarar mata,`yan wasa Gao Lin da Huang Sui sun zama zakaran gasa ta tsakanin mata biyu biyu.

Ran 23 ga wata da dare,a filin wasan motsa jiki na birnin Shanghai na kasar Sin,an kawo karshen gasar ba da kyautar zinari ta gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ta shekara ta 2006,dan wasa Liu Xiang daga kasar Sin ya lashe dan wasa Allen Johnson daga kasar Amurka da dakika 13.07,ya zama zakaran gasar gudun tsallake shinge na mita 110.

Ran 24 ga wata,an kawo karshen budaddiyar gasa ta wasan kwallon tebur wadda aka shafe kwanaki 4 ana yinta a kasar Japan,`dan wasa Wang Liqin daga kasar Sin ya zama zakaran gasa ta maza,`yan wasa Ma Lin da Wang Hao daga kasar Sin sun zama zakaran gasa ta tsakanin maza biyu biyu.`yar wasa Wang Yuegu daga kasar Singapore ta zama zakarar gasa ta mata.

Ran 23 ga wata,a karon karshe na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kwando ta mata ta 15,kungiyar kasar Austrelia ta lashe kungiyar kasar Rasha da ci 91:74,kuma ta zama zakara ta gasar,kungiyar kasar Rasha ta zama lambatu,kungiyar kasar Sin kuwa ta zama lamba ta sha biyu. (Jamila Zhou)