Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-26 19:09:39    
Jin dadin zaman rayuwar masunta a birnin Yuyang na lardin Shandong

cri

Yanzu lokacin zafi ya wuce, lokacin kaka ya yi a nan kasar Sin. Mutane da yawa sun nuna sha'awar dauka amfanin teku a bakin teku da kuma kama kifi tare da masunta, suna son fahimtar zaman rayuwar masunta. Yau ma za mu gabatar muku da wani wuri, inda mutane za su ji dadin yawon shakatawa a bakin teku, sunansa Yuyang, da ke lardin Shandong na gabashin kasar Sin.

Birnin Yuyang yana karkashin shugabancin hukumar birnin Yantai. Birnin Yuyang yana kusa da birane 3, wato birnin Yantai yana arewacinsa, birnin Weihai a gabas, kuma birnin Qingdao a yamma, wadanda suka shahara ne a fannin yawon shakatawa. Tsawon lokacin da ake dauka wajen zuwa wadannan birane 3 daga birnin Yuyang ya wuce awa 1 kawai. Saboda haka, a lokacin da suke tsara ajandar yawon shakatawa, mutane da yawa sun fi son kai wa wadannan birane 4 ziyara tare.

Yuyang sabon birni ne wajen yawon shakatawa, in an kwatanta shi da wadannan birane. Rairayin bakin teku mai launin rawaya iri na zinare da fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 10 ya dauke ido sannu a hankali tun daga tsakiyar shekaru 1980. An fara gina manyan dakuna masu kyaun gani a cikin yankin shakatawa tun bayan da shekaru 1990. A sakamakon haka, Yuyang ya kan ba masu yawon shakatawa mamaki domin kyaun gani da shiru da kuma kwanciyar hankali.

Yin kwana a cikin gidajen masunta da cin abincin teku a cikin jiragen ruwa da kama kifi tare da masunta harkokin yawon shakatawa ne na musamman da hukumar birnin Yuyang ta shirya bisa halin musamman na aikin su a kan teku, masu yawon shakatawa sun nuna sha'awa sosai.

A idanun mutanen da ke zama a bakin teku, kawowa da janyewar ruwan teku sun zama harkokin yau da kullum, amma a idanun masu yawon shakatawa da ba safai su kan je bakin tekun ba, ko da yin hira da masunta a bakin teku, sun ji mamaki da zumudi sosai.

Masu yawon shakatawa sun kan sayi danyun kifayen da masunta suka kama ba da dadewa ba a bakin teku. Suna alla-alla wajen cin danyun abincin teku. Masuntan wurin su kan tuki jiragen ruwansu tare da masu yawon shakatawa, su kama kifaye tare.

Ban da wannan kuma, masu yawon shakatawa suna son dauka amfanin teku a kan rairayin bakin teku. A lokacin janyewar ruwa, mutane sun dauka kananan kifaye da jatan lande da bawon kifi da dai sauran makamantansu a kan rairayin bakin teku.

Ga shi, wata budurwa mai suna Zhang Fan tana neman samun amfanin teku a cikin ramukan duwatsun teku a tsanake. Ta ce'Na samu wasu kananan seaf lowers, hakan wadannan kananan seaf lowers daga ramukan duwatsun teku yana da wuya, saboda su ne bawon kifi, da zarar na taba su, sun janye jikinsu. Ban da wannan kuma, na sami wani babban clam, girmansa ya kai wani dunkulallen hannu mutum. Lokacin da nake yawon a kan rairayin bakin teku, na gano shi, daga baya na haka shi daga karkashin rairayi.'

Bayan janyewar ruwan teku, akwai makwancin ruwan teku da dama a tsakanin ramukan duwatsun teku, inda ko da yake babu ruwa da yawa, amma akwai amfanin teku iri daban daban. Kaguwoyi su kan buya a karkashin kananan duwatsu. Mutanen sun ji dadin dauka amfanin teku a kan rairayin bakin teku. Zhang Fan ta kara da cewa, 'Mu kan zo rairayin bakin teku mu dauka amfanin teku a karshen mako tare da abokaina. Mun ji dadin kallon teku da jin wakokin igiyar ruwan teku. Rairayin yana da taushi, yana da dadin takawa. Saboda haka, mutanen da ba birninmu ba da yawa su kan yi yawon shakatawa a nan.'

Wannan gaskiya ne kamar yadda Zhang Fan ta fada, rairayin bakin teku na Yuyang ya yi suna sosai. Mutane da yawa su kan yi yawo a bakin teku a ko wace rana.

Mr. Wu Sheng da ya zo daga lardin Anhui ya je Yuyang don fahimtar zaman rayuwar masunta a karo na farko, ya ji matukar farin ciki. Ya ce, 'Mun zo ne daga lardin Anhui. Wannan bakin teku ya faranta mana rayuka sosai, akwai wurare masu ni'ima a nan, kuma mutanen wurin suna da kirki.'