Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, wanda ya kan sha kofi ya fi saukin karbar ra'ayoyi na sauran mutane, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan yin watsi da shan taba. To, yanzu ga bayanin.Bisa sabon nazarin da aka yi, masu ilmin kimiyya sun gano cewa, wanda ya kan sha kofi ya fi saukin karbar ra'ayoyin sauran mutane da suka gabatar. Ina dalili? Ko sabo da idan an sha kofi, sai za a ji farin ciki? A'a, ba haka ba ne, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan an sha kofi, to harkokin kwakwalwa suna gudana sosai tare da kallafa rai.
Bisa labarin da muka samu daga mujallar Sabbin Masu Ilmin Kimiyya ta kasar Birtaniya, an ce, manazarta na jami'ar Queensland ta kasar Australia sun bayyana cewa, wanda ya kan sha kofi yadda ya kamata ya fi saukin karbar ra'ayin da ya sha bamban da nasa. Don me? Sabo da bayan da aka sha kofi, zai ji farin ciki? Ko akwai sauran dalilai?
Domin fahimtar batun, manazarta sun yi wa mutane 150 jarrabawa. Da farko, an yi musu wasu tambayoyi masu muhimmanci sosai kamar ko suna so a yi musu allurar mutuwa idan su kamu da ciwon da ba a iya warkewa ba ko a'a, daga baya kuma an ba su abin sha iri biyu, daya shi ne abin sha da ke hade da caffein milligram 200, saura dayan kuwa abin sha maras caffein. Bayan mintoci 40, wato lokacin da yawan caffein da ke cikin jininsu ya fi yawa, an gaya musu wasu ra'ayoyin da suka sha bamban da nasu. A karshe dai an gano cewa, mutanen da suke sha abin sha da ke hade da caffein sun fi saukin karbar ra'ayoyi na sauran mutane.
Domin ci gaba da tabbatar da dalilan da ya sa mutane suka karbar ra'ayoyin da suka sha bamban da nasu, wato sabo da suna farin ciki? Ko sabo da harkokin kwakwalwarsu suna gudana sosai tare da kallafa rai? Manazarta sun yi wasu jarrabawa daban , kuma sakamako ya nuna cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da harkokin kwakwalwarsu suna gudana sosai tare da kallafa rai. Ban da wannan kuma manazarta suna ganin cewa, caffein yana sa mutane su fi mai da hankali a kan abubuwan da aka fada, ta yadda za su fi saukin karbar ra'ayoyi na sauran mutane.
Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan yin watsi da shan taba. A ko wace shekara, mutane kusan miliyan biyar suna mutuwa sakamakon ciwace-ciwacen da ke da nasaba da shan taba. Wadanda su kan shan taba da yawa suna fatan za su iya yin watsi da ita, amma wasu da ke cikinsu kawai sun ci nasara. To yanzu bari mu gabatar muku da wasu dabaru kan yin watsi da shan taba.
|