Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-25 22:14:22    
Kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa wajen horar da ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci

cri

A ran 23 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, a nan birnin Beijing, ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci da suka zo daga kasashe masu tasowa 23 sun gama karatunsu fiye da wata guda da kawarrun kasar Sin suka koyar musu, yanzu suna yin amfanin da sabbin fasahohin da suka samu wajen bayar da gudummowa a kasashensu. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan horon da aka bayar musu wajen sa ido kan ingancin abinci.

Wadannan ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci na kasashe masu tasowa sun zo nan birnin Beijing ne a farkon watan Yuli na shekarar da muke ciki domin karbar horon da bangaren Sin ya ba su. Ma'aikatan sun zo daga kasashen Albania da Cuba da Ecuador da Burma da Vietnam da Niper da kuma Philippines da dai sauransu, kuma yawansu ya kai 32 gaba daya. Lokacin da suke birnin Beijing, sun shiga kwas din horaswa ta kasa da kasa wajen fasahohin sa ido kan ingancin abinci da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta shirya don tallafa wa kasashe masu tasowa. Kwararrun kasar Sin da suka ba da darussa ba kawai suka yi cikakken bayani ga wadannan ma'aikata kan fasahohi da kayayyaki da kasar Sin ke yin amfani da su a fannin dudduba ingancin abinci ba, har ma sun bayyana yadda kasar Amurka da kuma kungiyar tarayyar Turai suke bincike da kuma tabbatar da abinci na halitta da na canzawar kwayoyin halitta wato 'Gene', bugu da kari kuma an shirya musu wasu harkokin bincike a jere.

A ran 23 ga watan Agusta, an yi bikin sauke karatu na wannan kwas din horaswa bayan da aka gama dukkan darussan da aka tsara. Wani jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ya halarci bikin ya bayyana cewa, bangaren Sin yana ganin cewa, wannan kwas din horaswa ya cimma makasudin da aka yi.

Chen Xuezhong, mai kula da ayyukan horaswa ya gaya wa wadannan ma'aikata cewa, kasar Sin tana son yin musanyar sakamako mai kyau da ta samu tare da sauran kasashe kan dudduba ingancin abinci. "ina fatan darussan da muka shirya za su ba da taimako ga kasashen nan wajen bunkasuwar fasahohin dudduba ingancin abinci, ban da wannan kuma ina fatan kwas din horaswa zai zama wani dandalin musanyar fasahohin dudduba ingancin abinci tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a yada fasahar kasar Sin wajen dudduba ingancin abinci zuwa kasashe masu yawa da ke bukatar fasahar."

Haka kuma Mr. Chen ya nuna cewa, a cikin shekarun nan da suka gabata, aukuwa da yaduwar cutar haukan shanu da ta kafa da baki sun yi mumunar illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar duniya, sabo da haka an shigad da batun ingancin abinci a cikin muhimman batutuwan da kasashe daban daban suke tattaunawa, kuma kasashe masu yawa ciki har da kasar Sin sun tsara dokoki da ka'idoji da yawa na fasahohin dudduba ingancin abinci.

Bugu da kari kuma, Mr. Chen ya bayyana cewa, yanzu, kasar Sin tana yin kokari domin kara kyautata tsarinta na dudduba ingancin abinci, a waje daya kuma tana so ta taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen horar da ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci da kuma yin musanyar sakamako mai kyau da kuma darasi da kasar Sin ta samu a wannan fanni. Haka kuma ya bayyana cewa, ma'aikatan da yawa da suka shiga wanan kwas din horaswa sun bayyana burinsu na hadin gwiwa tsakaninsu da bangaren Sin a fannin dudduba ingancin abinci, kasashen Benin da Vietnam da Burundi da sauran kasashe kuwa sun sa hannu a kan takardun nuna niyyar yin hadin gwiwa tare da bangaren Sin.

Malam Sakiusa Biaukula na ma'aikatar noma ta kasar Fiji ya nuna godiya ga kasar Sin da ta shirya irin wannan horo. "bisa matsayinta na wata kasa mai tasowa, fahasar kasar Fiji wajen dudduba ingancin abinci yana baya idan an kwatanta ita da ta kasar Sin da sauran kasashe. A wannan karo, kasar Sin ta shirya kwas din horaswa mai muhimmanci sosai domin taimaka wa kasashe masu tasowa kamar kasar Fiji wajen daga matsayinsu na fasahar, kasar Fiji tana so ta yi amfani da wannan zarafi domin koyon sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu."

Bugu da kari kuma, Malam Kiyuku Prosper da ya zo daga jami'ar Burundi ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da ya shiga kwas din horaswa da gwamnatin kasar Sin ta shirya, kuma ya samu karuwa da yawa bisa sanadiyar karatunsa a kasar Sin, "an shirya lacca da kyau kwarai da gaske, masu ba da lacca su kwararru ne a fannin dudduba inganci abinci, kuma kayayyakin duddubawa da aka nuna mana suna da zamani, ina jin mamaki ga dukkan wadannan abubuwa sosai. Na yi imani cewa, za a daga matsayina da na sauran ma'aikata wajen dudduba ingancin abinci ta kwas din horaswa."

A gun bikin sauke karatu, ma'aikata masu yawa sun bayyana cewa, za su yi amfani da sabon ilmin da suka koya a cikin ayyukansu domin daga matsayin kasashensu wajen dudduba ingancin abinci. Kande Gao)