Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-25 22:05:51    
Kabilar Buyi

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kananan kabilun kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Buyi ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: kasar Sin ta karfafa kare kayayyakin tarihi na kananan kabilun Sin.

An fi samun 'yan kabilar Buyi a shiyyoyi biyu na kabilun Buyi da Miao masu cin gashin kai da ke kudancin jihar Guizhui da kudu maso yammacin jihar ta kasar Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Bai ya kai miliyan 2.9. 'Yan kabilar Buyi suna yin amfani da harshensu, wato harshen Buyi. Kafin kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kabilar Buyi ba ta da harafinta, har kullum suna yin amfani da harafin kabilar Han, bayan kafuwar kasar Sin, an kago harafin kabilar Buyi bisa tushen harafin Latin.

Bayan kafuwar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin, 'yan kabilar Buyi sun yi gyare-gyare kan zamantakewar al'umma a jere don kau da tsarin mallakan filaye irin na 'yan jari hujja. Daga baya kuma, an gama yin gyare-gyare na gurguzu kan masana'antu da kasuwanci. Bisa manufofin kananan kabilu da gwamnatin Sin ke aiwatarwa, 'yan kabilar Buyi sun gudanar da harkokin kansu a shiyyar da suke ciki. Ya zuwa yanzu shiyyar kabilar Buyi ta riga ta yi sauye-sauye sosai. Alal misali, kafin kafuwar kasar Sin, ko kusa ba a iya samun masana'antu a shiyyar kabilar Buyi ba, amma bayan kafuwar kasar Sin, an kafa masana'antu na karfe da wutar lantarki da saka da sukari da sarrafa abinci da sauransu, ta haka jimlar masana'antu na shiyyar ta samu karuwa cikin sauri sosai. Ban da wannan kuma an raya sha'anin rini na kabilar Buyi sosai, bayan kafuwar kasar Sin, an kafa masana'antar rini ta birnin Anshun, zannuwan da masana'antar ta saka sun shahara a cikin gida da waje. Ana iya sayen zannuwan nan a Japan da kudu maso gabashin Asiya da Afirka da kuma Latin Amurka.

Bugu da kari kuma, an bukasa sha'anin ba da ilmi da kiwon lafiya cikin sauri, yanzu kusan dukkan yara suna iya shiga firamare, a wasu wurare kuwa, an kafa makarantun sakandare da na koyar da sana'o'i. Game da aikin kiwon lafiya, gwamnatin kasar Sin ta samar da kayayyki da mutane da kuma kudi domin ba da taimako ga 'yan kabilar Buyi wajen raya sha'anin kiwon lafiya, ta yadda aka ba da tabbaci ga lafiyar 'yan kabilar.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin ta karfafa kare kayayyakin tarihi na kananan kabilun Sin.