Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-25 19:08:25    
Kasashen Afirka suna matukar bukatar taimako daga kasashen duniya wajen yaki da ciwon tibi

cri
Wasu kwararru da kungiyoyin ba da taimako don yaki da talauci sun yi kira a kwanan baya cewa, tilas ne hukumomin kasa da kasa su kara mai da hankulansu da kuma kara ba da taimako wajen shawo kan ciwon tibi, in ba haka ba, yaduwar irin wannan mummunan ciwo a kasashen Afirka za ta kawo babban hadari.

Wata kungiyar duniya da ke himmantuwa kan kawar da talauci ta ba da wani rahoto a kwanan baya cewa, kudaden da Bankin Duniya ya bayar wajen shawo kan ciwon tibi a kasashen Afirka sun yi kadan sosai.

Rahoton ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, Bankin Duniya ya kebe kudin da yawansa bai kai kashi 5 cikin dari ba ga kasashen Afirka wajen shawo kan ciwon tibi, in an kwatanta da jimlar kudin da ya kashe a duk dunya. Wato ko wane dan Afirka mai fama da ciwon tibi ya sami kudin taimako na cent na kasar Amurka 80 kawai wajen warkar da wannan ciwo, amma ko wane mutum na sauran wuraren duniya da ke fama da wannan ciwo ya iya samun kudin taimako na dalar Amurka 9.4.

Ban da wannan kuma, Bankin Duniya bai rarraba kudin taimako da ya kashe wajen kiwon lafiya a kasashen Afirka cikin daidaituwa ba. Ya yi amfani da kudin da yawansa bai kai kashi 1 cikin dari ba wajen shawo kan ciwon tibi a shekarar 2005 da ta gabata, amma kudaden da ya kashe wajen shawo kan zazzabin cizon sauro da ciwon kanjamao sun yi yawa.

Yanzu kasashen Afirka suna fuskantar hali mai matukar tsanani a fannin ciwon tibi. A lokacin da kasashen duniya suke samun ci gaba sannu a hankali, amma Afirka wata nahiya ce kawai inda yawan mutanen da suka kamu da ciwon tibi yake karuwa, yawan mutane masu kamuwa da irin wannan ciwo yana karuwa da kashi 5 cikin dari a ko wace shekara. Adadin da abin ya shafa ya nuna cewa, yawan mutanen kasashen Afirka ya kai kashi 13.8 cikin dari bisa na dukan mutanen duniya, amma yawan mutanen da ke fama da ciwon nan ya kai kashi 25 cikin dari bisa na dukan masu fama da wannan ciwo na duk duniya. A ko wace shekara a kasashen Afirka, yawan masu fama da ciwon tibi da za a kara ya kai miliyan 2 da dubu dari 4, sa'an nan kuma, mutane fiye da dubu dari 5 suna rasa rayukansu a sakamakon irin wannan ciwo.

Ba za a iya raba wuyar shawo kan ciwon tibi daga dinbim mutane masu kamuwa da ciwon cutar AIDS a kasashen Afirka ba. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, sulusin mutanen da suka kamu da cutar AIDS sun rasu a sakamakon ciwon tibi. Yawan karuwar mutanen da suke kamuwa da ciwon tibi a kasashenn Afirka a ko wace shekara ya kai kashi 3 cikin dari, matsakaicin irin wannan yawan karuwa ta duk duniya ya kai kashi 1 cikin dari kawai, dalilin da ya sa haka shi ne domin kamuwa da ciwon kanjamao da ciwon tibi tare.

Sa'an nan kuma, kwayoyin cutar tibi suna kara jure magani a Afirka yanzu. A kwanan nan, an samu wani kwayar cutar tibi da ke fi jure magani a kasar Afirka ta Kudu, har yanzu mutane ba su sami magani mai amfani da zai iya shawo kan irin wannan kwaya ba.

Ciwon tibi ciwo ne da ke da nasaba da talauci. A kasashen Afirka, mazaunan gidajen bayan gari masu yawa suna fuskantar karancin manyan gine-ginen kiwon lafiya da kazanta da kuma dinbim mutane, bayan kamuwa da ciwon tibi, ba su da kudin ganin likita. Kamuwa da ciwon ya sanya mutane da yawa su rasa kwarewar aiki, ta haka talauci ya kara tsananta.

A lokacin da ake yin dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya a birnin Davos na kasar Switzerland a watan Janairu na wannan shekara, kungiyar kula da shirin hadin gwiwa wajen kawar da ciwon tibi, wadda ke karkashin shugabancin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, ta sanar da wani shiri, wato za a rage masu fama da ciwon tibi na duk duniya da rabi a shekarar 2015. Yanzu ana bukatar dalar Amurka biliyan 31 don cika wannan makasudi, kasashen Afirka kuma suna bukatar taimakon kudi na dalar Amrka a kalla biliyan 10.

Jami'in kula da wannan shiri ya bayyana cewa, yanzu gwamnatocin kasashen Afirka suna yin iyakacin kokarinsu, amma dole ne kasashen duniya su kara ba su tallafawa.(Tasallah)