Ran 21 ga wata, Mahmud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran da ke halartar babban taron M.D.D. na 61 a birnin New York, ya bayyana cewa, kasar Iran tana aiwatar da shirin nukiliya ne domin zaman lafiya, kasar Iran ba ta bukatar boma-boman nukiliya.
A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. Ahmadinejad ya ce, kasar Iran tana son ci gaba da yin shawarwari da kungiyar tarayyar kasashen Turai dangane da matsalar nukiliya ta Iran, kuma za ta iya dakatar da ayyukan inganta sinadarin uranium bisa sharadin "daidaituwa da adalci". (Bilkisu)
|