Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-22 16:47:44    
Ana raya aikin noma na zamani a kauyukan birnin Xi'an na kasar Sin

cri

Birnin Xi'an shi ne fadar gwamnatin lardin Shaanxi da ke a arewa maso yammacin kasar Sin. A duk lokacin hutu, 'yan birnin su kan runtuma, su tafi gandayen noma da ke zagayen birnin don dibar 'ya'yan itatuwa da sauran amfanin gona kamar yadda manoma ke yi, sa'an nan su more rayuwarsu ta hanyar samun iska mai tsabta da kyakkyawan muhalli mai ban sha'awa da sauransu. Su ci kayayyakin lambu da na marmari, su more rayuwarsu irin rayuwar da ba su iya samu a birni. Ta haka, yawan kudin shiga da manoman kauyukan birnin ke samu ma yana ta karuwa sannu a hankali ta hanyar hidimar da suke yi wa 'yan birni.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ana ta kokari wajen raya aikin noma na zamani a kauyukan birnin Xi'an ne, ba ma kawai don samar da amfanin gona ga 'yan birni ba, hatta ma don samar musu da wuraren yawon shakatawa.

A wani kauye mai suna "Weiyang" da ke zagayen birnin Xi'an, akwai wani gandun noma, inda aka dasa bishiyoyi masu ba da wani irin 'ya'ya da ake kira "Peach" a Turance a filaye masu fadin kadada sama da 1000. A yanayin bazara, yayin da furannin bishiyoyin suka tohu sosai, sai 'yan birnin masu dimbin yawa suna ta zuwa gandun noman don more idonsu da furannin. Da Madam Huang Xiao, mataimakiyar shugabar wannan gandun noma ta tabo magana a kan gandunta, sai ta bayyana cewa, "mun fara dashe-dashen bishiyoyi masu ba da 'ya'yan "Peach" a gandunmu ne a shekarar 1986. Yanzu, fadin filayen da muka dasa bishiyoyin ya riga ya wuce kadada 1000, yawan kudi da mu kan samu daga wajen sayar da "Peach" na ko wace kadada ya iya kai kudin Sin Yuan 75,000 zuwa 120,000 a ko wace shekara, wato ya tashi daidai da Naira na Nijeriya miliyan 1 da dubu 125 zuwa miliyan 1 da dubu 180. Ka zalika mu kan shirya bikin dibar "Peach", musamman domin 'yan birni a ko wace shekara, a lokacin bikin, 'yan birnin masu dimbin yawa su kan runtuma su zo gandunmu don halarci bikin da sauran harkokin yawon shakatawa."

Yanzu, an fara samun sakamako mai kyau wajen bunkasa aikin noma ta hanyar zamani a kauyuka da ke zagayen birnin Xi'an. Manoman kauyukan suna ta kara cin gajiyar hanyar zamani da suke bi wajen yin aikin noma.

A wani kauye daban mai suna " Xibashi" da ke zagayen birnin Xi'an, manoma suna amfani da takin gargajiya wajen noma kankana mai zaki kwarai, wadanda suka samu karbuwa sosai daga wajen masaya. Malam Gong Kanghai, dagacin kauyen ya bayyana cewa, "ana ta sanya ido ga aikin noman kankana da manoman kauyensa ke yi, tun lokacin da suka fara renon irinta har zuwa lokacin da ta nuna. Wajibi ne, manoman su yi amfani da takin gargajiya wajen noman kankana, haka kuma magungunan kashe kwari da suke amfani da su ma ba su gurbata muhalli. "

A kauye mai suna Baqiao da ke zagayen birnin Xi'an, kungiyar 'ya'yan itatuwa da ake kira "Cherry" a Turance ta kan shirya bikin dibar 'ya'yan itatuwa irin na "Cherry" musamman domin gwada wa 'yan birni 'ya'yan itatuwan nan masu dadin ci. A gun bikin, manoma su kan yi wake-wake da raye-raye don nuna yabo ga kungiyar bisa taimako da take yi musu.

Yanzu, an riga an kafa gandayen noma da fadinsu ya wuce kadada dubu goma a kauyuka da ke zagayen birnin Xi'an. Yawan iyalan manoma da ke aiki a wadannan gandayen noma ya kai dubu 500. Wasu amfanin gona da suke samu sun shahara a gida da waje. (Halilu)