Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-22 16:44:05    
Zantawa kan taron wasannin Olympic na Beijing daga wakili mai mukamin minista a ofishin jakadan Japan dake nan kasar Sin

cri

Kimanin shekaru biyu da suka yi saura ke nan da za a gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008. Lallai wannan gagarumin taron wasanni ya jawo hankulan kasashe mafi yawa a duniya. Kwanakin baya dai, wakilin redionmu ya ziyarci Mr. Ide Keiji, wakili mai mukamin minista a ofishin jakadan kasar Japan dake nan kasar Sin don ya fadi albarkacinsa kan wannan taron wasanni, inda ya nuna kyakkyawan fatan alheri ga gwamnatin birnin Beijing saboda ya samu damar gudanar da wannan gagarumin taron wasanni; Ban da wannan kuma Mr. Ide Keiji ya nuna kulawa sosai kan sauye-sauyen da kasar Sin za ta yi sakamakon samun damar gudanar da wannan taron wasanni.

A gun ziyarar, Mr. Ide Keiji yana zaku sosai bisa taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Ya yi farin ciki da fadin, cewa: ' gudanar da taron wasannin Olympic, wata babbar dawaiya ce. Lallai akwai ayyuka da yawa da jama'ar birnin Beijing da na duk kasar Sin za su yi. Ina fatan za su iya gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic dake gamsar da kowa'.

Mr. Ide Kaiji wanda yake zama a nan Beijing cikin shekaru biyu ya furta, cewa gagarumin taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing, ya kasance wani kasaitaccen taro ne da ya cancanci Japanawa dake aiki a kasar Sin suka zura masa ido. Yayin da yake more zaman jin dadin wasannin motsa jiki, Mr. Ide Keiji ya kuma mai da hankali sosai kan sauye-sauyen da kasar Sin za ta yi ta hanyar shirya taron wasannin Olympic. Ya fadi, cewa ' Yin musayar ra'ayoyi tare da Sinawa da kuma fahimtarsu yana da ma'ana gare ni.'

Yayin da Mr. Ide Keiji yake tabo magana kan taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008, ya yi waiwayen taron wasannin Olympic na Tokyo a shekarar 1964. Ya fadi, cewa: ' a wancan lokacin, ni wani dan makarantar firamare ne. Na yi kallon gagaruman gasanni ta T.V ; kuma wancan lokaci, lokaci ne da kasar Japan ta fi samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar yayin da take yin cudanya tare da kasashen ketare'.

Game da tasirin da mai yiwuwa ne taron wasannin Olympic na Beijing zai janyo wa dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan, Mr. Ide Keiji ya yi fatan masu sha'awar wasannin motsa jiki na kasashen biyu za su sa kaimi ga 'yan wasa na bangarorin biyu wato Sin da Japan. Ya kuma kara da ,cewa a lokacin da yake kallon hadaddiyar gasa ta wasan kwallon tebur ta kasar Sin, ya taba sa kaimi ga 'yar wasa Bajapaniya mai suna Fukuhara wadda take yin aiki a kungiyar lardin Liaoning. Sa'annan Mr. Ide Keiji ya ce, kasashen Japan da Korea ta Kudu sun hada kansu wajen gudanar da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a shekarar 2002. Kafin a soma yin gasar, mutane sun yi shakkar cewa ko za su iya gudanar da wannan gagarumar gasa da kyau ? Amma, a karshe dai, jama'ar kasashen biyu sun hada gwiwarsu sosai wajen gwada wata kasaitaccciyar gasa a gaban jama'ar duniya.

A sa'I daya kuma, Mr. Ide Keiji ya yi hasashen, cewa a lokacin da ake shirin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing, ya kamata kungiyoyin wakilan kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa da kuma musanye-musanye. Ya furta, cewa a da, marigayi Daimatsu Hirofun, shahararren malamin koyarwa na kasar Japan ya taba horar da 'yan wasan kwallon boli na mata na kasar Sin, ya kuma yi ayyuka da dama gare su, wadanda daga baya suka fi nuna rawar gani har suka samu haskakkun nasarori a cikin jerin gasannin da aka yi cikin zazzafan hali. Lallai wannan labari ya zama abun faranta rai ne a cikin tarihin musanye-musanyen da kasashen Sin da Japan suka yi tsakaninsu a fannin wasannin motsa jiki ; ' Ban da wadannan kuma', in ji shi, ' malaman koyarwa na Japan sun ba da taimakonsu ga 'yan wasa na kasar Sin a fannin wasan judo da na kwallon gora wato base ball a Turance. Duk wadannan suna da amfani ga kara dankon aminci da yin koyi da juna tsakanin 'yan wasa na kasashen biyu.'

Mr. Ide Keiji ya yi yabo sosai ga kokarin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic da gwamnatin birnin Beijing take yi. A karshe dai, ya jaddada, cewa ko shakka babu taron wasannin Olympic na nakasassu shi ma yana da muhimmanci. Amma, a halin yanzu, nakasassu ba sa samun al'amuransu cikin sauki a nan Beijing. Lallai akwai ayyuka da yawa gwamnatin birnin Beijing za ta yi.( Sani Wang )