Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-21 18:36:49    
Sabon ministan kudin Amurka ya yi sharhi a kan batutuwan da ke daukar hankulan jama'a dangane da tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Amurka da Sin

cri

A karo na farko ne Mr.Henry Paulson ke yin ziyara a kasar Sin tun bayan da ya kama mukaminsa na ministan kudi na Amurka a watan Yulin da ya gabata. A matsayinsa na manzon musamman na shugaban Amurka, a jiya ran 20 ga wata, shi da mataimakiyar firaministan kasar Sin, Wu Yi, sun hada kansu sun sanar da fara aiki da tsarin shawarwarin tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka. A lokacin ziyararsa kuma, zai yi shawarwari tare da manyan jami'an kasar Sin dangane da muhimman batutuwan da ke jawo hankulan jama'a a fannin ciniki da tattalin arziki da ke tsakanin Amurka da Sin. Idan an kwatanta shi da tsohon ministan kudin Amurka, wannan sabon ministan kudi wanda ya fi fahimtar kasar Sin ya burge jama'a sabo da saukin kansa da kuma sha'awarsa ta yin abubuwa na hakika, a kan batutuwan darajar musanyar kudin Sin da rashin daidaicin ciniki da dai sauran batutuwan da suke daukar hankulan jama'a.

Saukin kan Mr.Paulson ya bayyana ne da farko daga ra'ayinsa dangane da darajar musayar kudin Sin. Har kullum, wasu 'yan siyasa da masana'antu na Amurka suke zargin gwamnatin kasar Sin da sarrafa darajar musanyar kudin Sin, wai da gangan ne take saukar da darajar kudin Sin, don neman sa kaimi ga fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje, kuma wai hakan nan an haddasa babban gibin kudin cinikin da ke tsakanin Sin da Amurka. sabo da haka, suke neman a daga darajar kudin Sin. Amma a ganin Mr.Paulson, 'kara shigar da darajar musanyar kudin Sin cikin kasuwanni' da kuma 'kara bude kofar harkokin kudi na kasar Sin' sun fi muhimmanci. A gun taron watsa labaru da aka shirya a jiya ranar 20 ga wata, a fili ne Mr.Paulson ya bayyana cewa, ana bukatar wani dogon lokaci wajen yin gyare-gyaren darajar musanyar kudin Sin sannu a hankali. Ya ce. 'kasar Sin tana bukatar wani tsari na tsai da darajar kudin musanya bisa kasuwanni. Amma dole ne kasar Sin ta kafa wata cikakkiyar kasuwar jari don cimma wannan buri, kuma dole ne ta bude tsarinta na harkokin kudi sosai tukuna. Amma ana bukatar wasu lokuta don kammala wadannan ayyuka.'

Ana ganin cewa, dalilin da ya sa Mr. Paulson ya dauki wannan matsayi shi ne sabo da fahimtarsa dangane da kasar Sin. Yayin da yake kan kujerar jagorancin kamfanin Goldmansachs wanda ya shahara a duk duniya, ya taba kawo ziyara a nan kasar Sin har sau sama da 70.

Batun rikicin ciniki shi ne wani abu daban da ke jawo hankulan jama'a dangane da cinikin da ke tsakanin Sin da Amurka. 'yan majalisar dattawa guda biyu na kasar Amurka sun gabatar da shirin karbar kudin kwastan da yawansa ya kai kashi 27.5% a kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar, a kan batun, Mr.Paulson ya ce, 'Ban yarda da wannan shiri na neman sa wa kayayyakin kasar Sin kudin kwastan ba, kuma ba na goyon bayan wannan aikin da ke nuna ra'ayin kariyar ciniki, kuma zan yi kokarin shawo kansu da su yi watsi da shirin.'

Moriya daya ita ce tushen hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka. Mr.Henry Paulson yana son yin amfani da tsarin shawarwarin tattalin arzikin da ke tsakanin Sin da Amurka, don daidaita sabanin ra'ayi da ke tsakaninsu, da kuma kulla hulda mai kyau ta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen biyu kamar yadda ya kamata. Ra'ayin mataimakiyar firaministan kasar Sin, Madam Wu Yi, shi ma ya zo daya da na Mr.Paulson a yayin da take sanar da fara aiki da tsarin nan na shawarwari tare da Mr.Paulson, ta ce,'Muna imani da cewa, kafa wannan tsari da aka yi zai amfana wa hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka a fannin tattalin arziki, haka kuma zai taimaka wajen kulla muhimmiyar huldar aminci da hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma zai kawo tasiri mai kyau kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kwanciyar hankali da kuma tsaro.'(Lubabatu)