|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-09-20 21:24:20
|
Kamata ya yi, bunkasa hulda a tsakanin bangarori biyu na yankin teku na Taiwan cikin lumana ya zama babbar manufa ce, in ji Mr Jia Qinglin
cri
 Ranar 20 ga wata, Mr Jia Qinglin, zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, ya kamata, a mayar da bunkasuwar hulda a tsakanin bangarori biyu na yankin teku na Taiwan cikin lumana bisa matsayin babbar manufa.
Mr Jia Qinglin ya yi wannan kalami ne, yayin da yake ganawa da shahararrun mata na Taiwan da Hong Kong da Macao, wadanda ke halartar taron akan harkokin musanya a tsakanin matan bangarori biyu na yankin teku na Taiwan. Ya kara da cewa, babban yanki da Taiwan dukansu na kasar Sin ne, neman zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa buri ne daya ga jama'ar bangarorin biyu ciki har da matansu. (Halilu)
|
|
|