Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-20 19:26:53    
Kasar Sin ta sami maki na A+ tun shigarta a WTO a shekaru biyar da suka wuce

cri

Tambayar da za mu amsa a yau ta fito ne daga hannun malam Baba Zubair, mazauni birnin Kano na jihar Kaduna na kasar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, shin wadanne ci gaba ne kasar Sin ta samu tun shigarta kungiyar kasuwanci ta duniya a shekara ta 2001? Masu sauraro, yau shekaru kusan biyar ke nan tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO. Kwanan baya, a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, an yi wani taron tattaunawa na kasa da kasa dangane da cikon shekaru biyar da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, to, a cikin shirinmu na yau, bari mu ji wadanne ci gaba kasar Sin ta samu daga bakin bangarori daban daban da suka halarci taron.

Tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, ta bi dokokin ciniki na kungiyar WTO sosai, kuma ta cika alkawaran da ta dauka. A cikin shekaru 5 da suka wuce, gaba daya ne masu zuba jari daga kasashen waje sun fitar da ribar da yawanta ya kai dallar Amurka biliyan 57 da miliyan 940 daga kasar Sin. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta shigo da kayayyakin da yawansu ya kai kimanin dallar Amurka biliyan dubu 2 da dari 4 daga kasashen waje. Ban da wannan, bisa adadin da bankin duniya ya bayar, an ce, tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, karuwar tattalin arzikinta ya bayar da taimakon da a kalla ya kai kashi 13% ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Yi Xiaozhun ya fadi haka ne a gun taron tattaunawa da ke tsakanin kasa da kasa dangane da cikon shekaru 5 da kasar Sin ta shiga WTO wanda aka yi a ran 6 ga wata a birnin Shanghai na kasar Sin. A ganinsa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya samar da manyan kasuwanni ga kasashe daban daban, kuma ya samar da zarafi ga masu zuba jari na kasashen, ya kuma samar da babban karfi ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karshen watan Yuni da ya gabata, bankunan waje 71 sun kafa hukumominsu a nan kasar Sin, wadanda suke iya gudanar da harkokin kudin Sin na RMB a birane 25 na kasar. Ban da wannan, an kuma kafa kamfanonin hadin gwiwar jarin Sin da na kasashen waje 23 na kula da asusu da kuma 7 na takardun shaidar kudi.

Bayan haka kuma, ya zuwa karshen shekarar 2005, gaba daya ne akwai kamfanonin inshora 82 a kasuwannin inshora na kasar Sin, kuma daga cikinsu kamfanonin inshora na kasashen waje sun kai 41, wadanda rassansu kuma suka kusanci 400, kuma kudaden da kamfanonin inshora din nan na kasashen waje suka samu ya riga ya dau kashi 3.9% daga cikin kudaden da aka samu a nan kasar Sin a fannin inshora.

Mr.Yi Xiaozhun ya kuma yi nuni da cewa, 'A cikin shekaru 5 da suka wuce, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin bunkasuwar tattalin arzikinta. Yawan mutanen da ke fama da talauci a shekara ta 2002 a nan kasar Sin ya kai kimanin miliyan 32 da dubu 90, amma ya zuwa shekara ta 2005, adadin ya fadi har zuwa miliyan 23 da dubu 650. A shekara ta 2001, kasar Sin ta zo na shida a duk duniya a fannin tattalin arziki, amma ta sami ci gaba har zuwa na uku a shekara ta 2005.'

A ran nan kuma, babban sakataren taron dandalin Asiya na Bo'ao, Long Yongtu shi ma ya bayyana cewa, shigar kasar Sin a kungiyar WTO ba ma kawai ta sa kaimi sosai ga raya tattalin arzikin kasashe masu ci gaba, haka kuma ya ciyar da tattalin arzikin kasashe masu tasowa gaba, ciki har da kasashen Afirka. Ya ce, 'A halin yanzu dai, yawan kayayyakin da kasar Sin take shigowa daga kasashen Afirka ya karu da ninki har 43 gaba daya, kuma saurin karuwarsa ya kai kashi 50% a kowace shekara.'

Ban da wannan, babban darektan kungiyar WTO, Pascal Lami, wanda ke bayyana kasar Sin a matsayin 'giwa' a cinikin duniya, shi ma ya halarci taron, a ganinsa, kasar Sin ta sami maki mai kyau na A+ bayan da ta shiga WTO. Ya ce, 'bayan da kasar Sin ta shiga WTO, ta tabbatar da karuwar tattalin arziki na kanta, a yayin da ta kuma cika alkawarin da ta dauka kamar yadda ya kamata. Ta bayar da babban karfi ga karuwar tattalin arzikin duniya. A sa'i daya, ya kuma nuna cewa, bayan da aka dakatar da shawarwarin Doha, kariyar ciniki ya sami farfadowa a shiyyoyi daban daban na duniya, shi ya sa kungiyar WTO ta kara muhimmancinta, kuma kamata ya yi kasar Sin ta kara ba da taimakonta a WTO. Ya kuma jaddada cewa, yanzu ba ma kawai ya kamata mu waiwayi ci gaban da kasar Sin ta samu bayan da ta shiga WTO ba, kuma ya kamata ta kara shiga harkokin WTO.'(Lubabatu)