Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-20 16:27:54    
Me ya sa ake kasa hana kasashe masu hannu da shuni su zubar da diddigar masana'antu a yankunan kasashe masu talauci

cri

Ran 18 ga wata, bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Cote d'Ivoire suka bayar, an ce gwamnatin kasar tana cigaba da yin binciken batun zubar da diddigar masana'antu mai guba da ya faru a birnin Abidjan na kasar, kuma a kwanan baya an gurfanar da mutane biyu 'yan asalin kasar Faransa wadanda ke aiki a kamfanin Tork na kasar Holland wanda ya diddigar zuba masana'antu mai guba.

An haifar da wannan al'amari ne saboda kamfanin Tork ya yi hayar wani jirgin ruwa mai daukar kayayyaki wanda ya zuba diddigar masana'antu mai guba da nauyinta ta kai Ton darurruka a wurare sama da 10 na birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire. Har zuwa yanzu, gas mai guba da diddigar ta baza ta riga ta kashe mutane 7, sauran mutane 24 suna asibiti soboda suka sha gas mai guba sosai, ban da haka kuma akwai sauran mutane fiye da dubu 37 da aka kai su asibiti saboda ba su ji dadi ba. Wannan al'amari ya haifar da wani hadarin siyasa, wato gwamnatin wucin gadi ta kasar ta yi murabus.

Wannan al'amari daya ne dake cikin al'amuran da suka faru kamar haka. Tun daga shekaru 80 na karni na 20, kasashe masu cigaba sun kafa dokoki da yawa wadanda ke bukatar kamfanoni da su dawo da diddigar da suka zuba. Sai dai, wasu kamfanoni sun fara zuba diddigar masana'antu zuwa kasashe masu tasowa na Afirka, da Asiya da kuma na Latin Amurka, domin rage yawan kudin da suka kashe wajen dawo da diddigar. A shekaru 90 na karni 20, yawan cinikayyar diddiga na kasashen duniya ya kai kamanin dolar biliyan 90, har zuwa sheakrar 2000, yawan cinikayyar diddiga ya kai dolar biliyan 500. bisa kididdigar da aka yi, an ce, kungiyar gammayar kasashen Turai ta sayarwa kasashen Afirka da Asiya da Latin Amurka diddiga mai guba mai nauyin Ton miliyan 110. Kasar Amurka tana da jiragen ruwa musamman fiye da 400 don jigilar diddiga mai guba.

A cikin shekarun baya, kasashen duniya sun cimma jerin yarjejeniyoyi. A watan Maris na shekarar 1989 a Basel na kasar Switzerland, kasashe fiye da 115 sun daddale "yarjejeniyar Basel" don sarrafa harkokin jigilar diddiga mai guba a tsakanin kasa da kasa. A watan Satumba na shekarar 1995 a Geneva na kasar Switzerland, kasashe kusan 100 sun daddale gyararren shiri na "yarjejeniyar Basel"?wato "yarjejeniyar hana fitowar diddiga mai guba". Kasashen Afirka da kungiyar gammayar Turai sun daddale yarjejeniyar Lome wadda ta tanadi cewa, kungiyar tana da nauyin dakatar da zuba diddiga mai guba zuwa kasashen Afirka. A shekarar 1991, kasashen Afirka sun daddale yarjejeniyar Bamako wadda ta tsai da kudurin dakatar da shigo da diddiga daga ketare.

Amma wannan bai hana yunkurin jigilar diddiga mai guba ba. Masu bincike suna ganin cewa, akwai dalilai da yawa. Da farko, yawan kudin kawar da diddiga ya fi na fitar da su zuwa ketare. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kudin da akan kashe wajen dawo da diddiga mai nauyin Ton daya ya kai dolar 400 zuwa 1000, idan an fitar da su, yawan kudin da za a kashe ya kai dolar 10 zuwa 40 kawai ko Ton daya.

Na biyu, da wuya za a iya tafiyar da yarjejeniyoyin. Ana ganin cewa, akwai membobin kasashe kashi daya da ke cikin kashi uku ba su iya tafiyar da ayyukansu ba. Yawancin kasashen wadanda ba su tafiyar da ayyukansu ba masu talauci ne, ba su da karfi sosai don kawar da diddiga.

Ba da haka kuma, yanzu, ana yin yawancin cinikayyar diddiga mai guba a boye. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, kashi 70 cikin kashi 100 na diddigar da kasashen Turai suka yi jigilanrsu zuwa kasashe masu tasowa ba bisa doka ba.

Wasu manazarta suna ganin cewa, yanzu fitowar diddiga da gurbacewar kayayyakin masana'antu sun riga sun zama muhiman hanyoyin da kasashen masu cigaba suke bi wajen kwace albarkatun muhalli daga kasashe masu tasowa. Ya kamata kasashe masu tasowa su dauki manufofi bisa ka'idar bunkasuwa mai dorewa. [Musa]