Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-20 15:50:43    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(14/09-21/09)

cri
Ran 17 ga wata, an kawo karshen gasanni na tsakanin maza na budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin. Dan wasan kasar Cyprus Marcos Baghdatis ya zama zakara a cikin gasa ta tsakanin namiji da namiji, wannan karo ne na farko da ya zama zakara a cikin gasannin da kungiyar ATP ta shirya. Mario Ancic da Mahesh Bhupathi sun zama zakaru a cikin gasa ta tsakanin maza biyu biyu. 'Yan wasa mata sun fara karawa da juna tun daga ran 18 har zuwa ran 24 ga wata.

Ran 17 ga wata, an kammala gasar ba da babbar kyauta ta wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta shekarar bana, inda 'yan wasan kasar Sin suka sami lambobin zinare a cikin gasa ta tsakanin mace da mace da kuma gasa ta tsakanin maza biyu biyu. Zhang Yining ta zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mace da mace, Wang Liqin da Hao Shuai sun zama na farko a cikin gasa ta tsakanin maza biyu biyu.

Ran 17 ga wata, a birnin Athens, babban birnin kasar Girka, an rufe gasar cin kofin duniya ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta karo na 10. Shahararren dan wasan kasar Sin Liu Xiang, wanda ya taba samun lambar zinare a cikin taron wasannin Olympic na Athens, ya sami lambar azurfa a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 ta maza da dakikoki 13 da motsi. Allen Johnson tsohon gwanin wasan kasar Amurka ya zama na farko da dakikoki 12 da motsi.

Ran 12 ga wata, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Tsalle-tsalle da Guje-guje ta Duniya wato IAAF ta gabatar da sakamakon binciken da ta yi wa 'yan wasa 227 masu shiga cikin gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta duniya da aka yi a Beijing a kwanan baya a fannin magani mai sa kuzari, dukan 'yan wasa 227 ba su sha magani mai sa kuzari ba. An yi gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta duniya a nan Beijing tun daga ran 15 zuwa ran 20 ga watan Agusta, an yi bincike kan 'yan wasa 227 wajen magani mai sa kuzari kafin gasa da kuma lokacin gasa. Wannan karo ne na farko da kungiyar IAAF ta yi bincike kan 'yan wasa masu yawan haka a fannin magani mai kuzari a gun gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta duniya.(Tasallah)