Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-20 15:49:02    
An daga matsayin budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ba tare da tangarda ba

cri
Budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin da ake yi a nan Beijing tun daga ran 9 zuwa ran 24 ga wata gasa ce mafi girma da kasar Sin ta shirya wa kwararrun 'yan wasan kwallon tennis a wannan shekara, ban da gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon tennis maza ta duniya wato ATP za ta shirya a karshen shekarar bana. Wannan shi ne karo na uku da aka yi wannan gasa a Beijing. Ko da yake an gamu da matsaloli da yawa, amma wannan sabuwar gasar duniya ta sami saurin ci gaba.

Babban manajan kula da budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin Mr. Zhang Junhui yana ganin cewa, budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ta sami saurin bunkasuwa daga fannoni daban daban. Da farko, kungiyoyi na kasar Sin ne suka shirya wannan gasa da kansu. Masana'antu masu jarin kasashen waje sun shirya wannan gasa kafin shekaru 3 da suka wuce, amma yanzu kamfanonin kasar Sin sun ja akalar aikin shirya wannan gasa. Na biyu, masana'antun kasar Sin sun kara sa hannu cikin wannan budaddiyar gasa ta hanyar ba da kudade domin wannan gasa. Na uku, kafofin yada labaru da yawa sun mai da hankulansu kan wannan budaddiyar gasar da ake yi a shekarar bana, ta haka mutane da yawa na kasashen duniya sun kara zura ido kan wannan gasa. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta sami babban ci gaba wajen gayyatar 'yan wasan duniya da su shiga wannan gasa da kuma kyautata ingancin 'yan kallo.

Saboda an yi budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin bayan budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Amurka, wadda ke daya daga cikin manyan budaddun gasannin wasan kwallon tennis na duniya 4, shi ya sa an kawo illa ga shahararrun 'yan wasa da suka zo nan kasar Sin bisa wani matsayi. Mr. Zhang ya bayyana cewa, da can sun nuna damuwa kan yawan 'yan kallo, amma a zarihi kuma, mutane da yawa sun zo kallon gasanni, wannan ya shaida cewa, an kyautata ingancin 'yan kallon kasar Sin sannu a hankali, sa'an nan kuma, ya kara inganta niyyar gayyatar 'yan wasa kwararru. Ya ce,'Mun dora muhimmanci kan gayyatar 'yan wasan kwallon tennis kwararru a shekarar bana, da can wasu sun nuna damuwa cewa, idan ba mu gayyaci Rafael Nadal da David Nalbandian, to, budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin za ta gamu da matsaloli. Amma a gaskiya kuma, sauran 'yan wasa masu karfi suna alla-allar shiga cikin budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin. Kada mu mai da hankalinmu kan ko ya shahara ko a'a kawai, a maimakon ko zai iya yin fintikau ko a'a. 'Yan wasan da muka gayyata a wannan gami sun fi gwada gwanintarsu, in an kwatanta su da wadanda aka gayyata a cikin gasanni na matsayi iri daya da na mu, har ma a cikin gasanni na matsayin gaba da na mu.'

Ko da yake wasu shahararrun 'yan wasa ba su zo nan birnin Beijing ba, amma a zahiri kuma sauran 'yan wasa da suka shahara sun shiga budaddiyar gasar da ake yi a wannan shekara. Shugaban kungiyar ATP Mr. Brad Drewitt ya yi bayani kan wannan cewa, wasu daga cikin 'yan wasa 10 mafi nagarta da ke cikin jerin sunayen 'yan wasa maza na kungiyar ATP sun zo nan don shiga wannan gasa.

A fannin 'yan wasa mata kuma, ban da wasu shahararrun 'yan wasa mata na kasashen waje, 'yan wasan kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi, wadanda zakaru ne a cikin manyan gasannin wasan kwallon tennis na duniya 4, da kuma gogaggiyar 'yar wasa ta farko ta kasar Sin Li Na, wadda ta zama ta 21 a cikin jerin sunayen 'yan wasa mata na duniya, su ma sun shiga budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin da ake yi a wannan shekara.

Saboda irin wadannan ci gaba da kasar Sin ta samu, Mr. Zhang ya yi imani sosai cewa, wasan kwallon tennis na kasar Sin yana samun bunkasuwa, ya ce,'Kasar Sin ta sami ci gaba sosai a fannin wasan kwallon tennis. Lokacin da ake yin wannan gasa a kasar Sin a karo na 1, kowa da kowa ya ji mamaki, shi ya sa a lokacin nan ko da yake ta jawo hankulan mutane, amma mutane da yawa ba su fahimci budaddiyar gasar ta wasan kwallon tennis ta kasar Sin sosai ba. Duk da haka yanzu 'yan kallo masu kishin wasan kwallon tennis sun mai da hankulansu kan wannan gasa, suna sabawa da ita, wannan ya alamta cewa, budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin tana samun kyautatuwa.'(Tasallah)