Bisa manufofin kasar Sin dangane da raya kamfanonin masu zuba jari, yanzu kamfanonin kula da harkokin zuba jari na kasar da kamfanonin QFII na kasashen waje suna kara taka muhimmiyar rawa a kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin.
Ya zuwa karshen watan jiya, yawan kamfanonin kula da harkokin zuba jari na kasar Sin ya kai 57, haka nan kuma kamfanonin QFII na kasashen waje wadanda suka sami damar gudanar da harkokinsu a kasar Sin ma ya kai 42. Yanzu, yawan hada-hadar kudi da wadannan kamfanoni ke mallaka ya kai kashi 30 cikin dari bisa duk hada-hadar kudi da ake saye da sayarwa a kasuwannin kasar Sin.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kamfanonin masu zuba jari na kasar Sin da kafamonin QFII na kasashen waje sun riga sun sami ci gaba da sauri a kasar Sin wajen gudanar da harkokinsu a kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin. (Halilu)
|