Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 16:00:15    
Kofar Zhengyang ta Beijing

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko dai za mu yi harin haske kan kofar Zhengyang da ke birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, daga bisani kuma, za mu karanta muku wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Yin hira da mutanen da suka zama a gabobin tabkin Baiyangdian'.

Kofar Zhengyang wani babban gini ne da aka gina da bulo, tsayinta ya kai mita 42, tana kudancin filin Tian'anmen, wanda ya yi suna ne a duk duniya saboda girmansa. Da can mutane sun gina katanga tare da kofofi 9 a kewayen birnin Beijing, amma saboda dalilai da yawa, kadan daga cikin wadannan kofofi suna ci gaba da kasancewa tsaye a nan Beijing, kofar Zhengyang na daya daga cikinsu.

An gina ta don tsaron birnin Beijing a shekarar 1421 a farkon zamanin daular Ming na kasar Sin. An gina kofofi 2 wato ta ciki da ta daga waje don kiyaye birnin Beijing. Tsarin gina kofofi 2 ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da abokan gaba. Ko da abokan gaba sun lalata kofa ta daga waje, amma sun fuskanci kofa ta ciki, ba su iya shiga cikin birni ba, sa'an nan kuma an iya kai musu hari daga dakunan da ke kan kofa ta ciki. An harbi kibiyoyi daga tagogi 94 da aka gina a kan wannan kofa a lokacin yaki.

An taba kone wannan kofa sau da dama kafin aka sake gina ta a shekarar 1914. Saboda an mayar da ita a matsayin tsohon gini na gargajiya, shi ya sa an yi mata kwaskwarima bisa yadda take a cikin shekarar 1914. Da can sarki ne kawai ya iya ketare kofar Zhengyang a lokacin da yake zuwa gidan ibada na Tiantan, inda a kan shirya bukukuwa don girmama Ubangiji, ta yadda zai ba da wadata.

An gina babbar fada ta harbar kibiyoyi a shekarar 1439, wadda ke da tagogi 82, inda aka iya harbar kibiyoyi. An kone ta a shekarar 1780 da ta 1849 daya bayan daya, amma an sake gina ta. A cikin shekarar 1900, an barnatar da kofar Zhengyang, kuma sojojin kasashen waje 8 mahara da suka hada da Birtaniya da Faransa da sauran kasashe 6 sun kone wannan babbar fada. An yi musu kwaskwarima bisa zanen da aka shirya a da.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, gwamnatin kasar Sin ta sake inganta kofar Zhengyang a shekarar 1952, ta yi kwaskwarima kan babbar fada ta harbar kibiyoyi a shekarar 1976, a shekarar 1977 kuwa, ta sake yin kwaskwarima kan wannan kofa. Saboda haka, yanzu kofar Zhengyang da babbar fada ta harbar kibiyoyi sun sake ba da haske nasu.(Tasallah)