|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-09-19 16:45:09
|
 |
An fara tafiyar da ayyukan yin mu'amala tsakanin matan gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan
cri
Ran 19 ga wata, a nan Beijing, an bude taron kara wa juna sani na yin mu'amala kan bunkasuwar matan da ke gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan a karo na 3, inda wakilai mata 1300 daga gabobin 2 da yankunan Hong Kong da Macao suka halarci wannan taro. Wannan ya nuna cewa, an fara tafiyar da ayyukan yin mu'amala tsakanin matan da ke gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan a hukunce.
Babban batun da za a tattauna a kai a cikin ayyukan yin mu'amala tsakanin matan gabobin 2 shi ne ' 'yan uwa mata za su hada kansu don neman samun bunkasuwa tare', za a kuma shirya tarurukan kara wa juna sani da bukukuwan sada zumunta. Manyan ayyukan sun hada da taron kara wa juna sani da yin mu'amala kan bunkasuwar matan da ke gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan a karo na 3 da dandalolin musamman 4 da ayyukan ganewa ido da ziyara da kuma bukukuwan sada zumunta iri daban daban da za a yi a biranen Beijing da Shanghai da lardin Fujian na kasar Sin.(Tasallah)
|
|
|