Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 15:52:02    
Mata da suke da aikin yi sun fi lafiya

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da wani bayani kan cewa, mata da suke da aikin yi sun fi lafiya. Daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Yadda aka shimfida hanyar dogo ta Qingzang.

Bisa wani sabon binciken da kasar Birtaniya ta yi, an ce, matan da suke da aikin yi yayin da suke kula da iyali da yaransu, ko da yake sun fi shan aiki da kuma karbar matsi mafi yawa daga zamantakewar al'umma, amma wannan zai ba da taimako wajen lafiyar jikinsu idan sun dade suke yin haka.

Bisa labarin da muka samu daga mujallar ciwon yaduwa da kiwon lafiyar jama'a ta kasar Birtaniya ta bayar, an ce, manazarta na sashen nazarin ilmin ciwon yaduwa da kiwon lafiyar jama'a na jami'ar London sun yi bincike kan mata 1200 da shekarunsu ya kai 15 zuwa 54 da haihuwa, daga baya kuma sun iske da cewa, yawan mata masu aikin yi da suke kamu da ciwo sakamakon kiba fiye da kima ya kai kusan kashi 23 cikin dari, amma game da mata marasa aikin yi, kuma suke gida domin kula da iyali da yaransu kawai, yawansu da ke kamu da ciwon ya kai kashi 38 cikin dari.

A cikin binciken, manazarta sun yi wa mata kimantawa kan halin lafiyar jiki da suke ciki ta hanyar amsa takardun tambayoyi wadanda suke hada da halin aikinsu da aurensu da kuma yaransu. A karshe dai an gano cewa, mata da shekarunsu ya zarce 54, ko da yake suna shan aiki yayin da suke kula da iyali da yaransu, amma sun fi lafiya idan an kwatanta su da mata marasa aikin yi.

Dr. Ann Marken da ta kula da binciken ta bayyana cewa, nazarin ya nuna cewa, matan da suke iya daidaita aiki da kuma daukar nauyi bisa matsayinsu na mahaifiya da mata suna da lafiyar jiki. Ban da wannan kuma ta ce, binciken ya nuna cewa, ya kamata mu goyi bayan mata wajen samun aikin yi yayin da suke ciyar da yaransu.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan hanyar dogo ta Qingzang. A ran 1 ga watan Yuli ne shekarar da muke ciki, hanyar dogo ta Qingzang, wato tsakanin jihohin Qinghai da Tibet na kasar Sin, wadda ta fi tsayi daga leburin teku a duniya ta fara yin gwajin sufurin fasinjoji. Lalle wannan wata babbar nasara ce da kasar Sin ta ci, sabo da da kyar sosai an shimfida hanyar. To, yanzu bari mu ga yadda aka yi aikin nan.(Kande)