Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 15:55:51    
Kasar Sin ta yi maraba ga dalibai da suke zo daga kasashen Afirka

cri

Tare da kara bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, bangarorin biyu suna kara hadin kai da yin mu'amala a fannin ilmi. Sai mu ga wani bayani da wakilinmu ya aikato mana daga kasar Kenya, wannan bayani yana da lakabi haka: kasar Sin ta yi maraba ga dalibai da suke zo daga kasashen Afirka.

A ranar 5 ga watan Satumba, wata tawagar ilmi ta kasar Sin da ta hada da kwamitin kula da asusun daliban kasashen waje na kasar Sin da wakilan da suka zo daga manyan jami'o'in kasar Sin ta shirya wani taro a jami'ar Nairobi ta kasar Kenya domin bayyana manufofin kasar Sin wajen daukar daliban kasashen Afirka.

A gun taron, ta hanyoyi daban daban na kafofin watsa labaru, wakilan da suka zo daga shahararrun jami'o'in kasar Sin sun bayyana manufofinsu wajen daukar daliban kasashen Afirka. Daliban Kenya da yawa sun halarci taron, sun yi tambayoyi, sun sami takardun bayanai. Sun kuma nuna sha'awa sosai a kan dalibta a kasar Sin.

Wani dalibi ya gaya wa wakilinmu cewa, 'Ina godiya domin jami'o'in kasar Sin sun zo nan sun shirya irin wannan taro. Ina farin ciki, idan zai yiyu, ina fata za a shirya irin wannan taro har sau biyu a ko wace shekara.'

Bisa kididdigar da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2005, yawan daliban kasashen Afirka da ke karatu a kasar Sin ya kai dubu 2 da dari 7 da 57, wanda ya karu bisa na da. Shirya bukukuwan dangane da ilmi a Afirka ya zama wata hanya mai amfani wajen biyan bukatun daliban Afirka da suke karatu a kasar Sin. Shugaban tawagar ilmi ta kasar Sin kuma mataimakin sakataren kwamitin asusun dalibai na kasar Sin Li Jianmin ya ce, tawagar kasar Sin ta isa kasar Kenya bayan da ta halarci bikin nune nunen fasahohin ilmi da aka shirya a karo na biyu a kasar Tanzaniya. Ya gaya mana cewa, 'tawagar ilmi ta kasar Sin ta fi girma a gun biki, sabo da haka, bangaren kasar Tanzaniya yana mai da hankali sosai a kan mu. Bisa kididdigar da muka yi, wakilan dalibai na tawagarmu sun riga sun gana da daliban Tanzaniya da yawansu ya kai dari 6 ko dari 7. Kashi 15 daga cikinsu sun ba mu sunayensu da hanyar yin mu'amala da juna, wannan ya bayyana cewa, suna fatan karatu a kasar Sin.'

Ban da wannan kuma, a cikin ko wace shekaru biyu, kasar Sin za ta shirya taron bayyana manufofin dalibta zuwa kasar Sin a kasar Massar da Afirka ta kudu, a watan Disamba na shekarar da muke ciki, kwamitin asusun dalibai na kasar Sin zai shugabanci wakilan da suke zo daga jami'o'in kasar Sin da yawansu ya kai kusan 50 zuwa Massar da Afirka ta kudu domin shirya taron bayyana manufofinsu.

Ban da taron bayyana manufofi, gwamnatin kasar Sin ta riga ta kara yawan daliban Afirka masu samun kudin tallafi a jami'o'in kasar Sin. Li Bing ta kwamitin asusun dalibai na kasar Sin ta gaya mana cewa, a cikin shekarar da muke ciki, yawan daliban kasashen waje masu samun kudin kyauta a jami'o'in kasar Sin ya riga ya kai dubu 10.

Dalibai 29 na kasar Kenya da suka samun kudin tallafi daga gwamnatin kasar Sin, za su zo kasar Sin nan ba da dadewa ba. Wani daga cikinsu mai suna Bitange Hipa Tochi ya gaya mana cewa, 'a halin yanzu, jama'ar Sin da Kenya suna kara kusanta da juna, gwamnatin kasar Kenya kuma ta tsara manufar 'mai da hankali a kan gabas', to, wadannan abubuwa biyu su ne manyan dalilan da suka sa na zabi kasar Sin don in zo in karatu a can.'(Danladi)