Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 16:04:46    
Mr. Baradei ya yi kira a warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari

cri
Ran 18 ga wata, a gun bikin bude zaunannen taro na karo na 50 da babban taron Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya wato IAEA ya shirya a birnin Vienna, babban darektan hukumar Mr. Mohamed El Baradei ya sake yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari.

Mr. Baradei ya kara da cewa, yana fatan kasar Iran da Kungiyar Tarayyar Turai da sauran bangarorin da abin ya shafa za su yi tattaunawa don samar da sharadi wajen yin shawarwari, ta yadda za a cika makasudi na warware matsalar nukiliya ta kasar Iran daga dukan fannoni, ban da wannan kuma, ya kamata a yi la'akari da ikon kasar Iran a fannin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. A sa'i daya kuma, Mr. Baradei ya yi suka ga kasar Iran saboda ba ta aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da shi ba, wato ba ta dakatar da ayyukan tace sinadarin uranium a cikin wa'adin da aka kayyade ba.

A wannan rana kuma, a birnin Caracas, shugaban kasar Iran Mr. Mahmud Ahmadinejad da ke ziyara a kasar Venezuela ya nanata cewa, kasar Iran tana mallakar ikon halak wajen yin amfani da makamashin nukiliya cikin ruwan sanyi da kuma yin bincike kan fasahar nukiliya.(Tasallah)