Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 14:45:26    
Gwamnatin Somali ta kama mutane 2 da ake zarginsu da laifin tayar da bom

cri
Ran 18 ga wata, gwamnatin kasar Somali ta tabbatar da cewa, hukumar tsaron kasar ta kama mutane 2 da ake zarginsu da laifin yunkurin kisan gilla ga shugaban rikon kwarya na kasar Mr. Abdullahi Yusuf Ahmed , wadanda suka tayar da boma-bomai a ran nan.

Ministan harkokin waje na gwamnatin wucin gadi ta kasar Somali ya bayyana cewa, yanzu hukumar tsaron kasar tana ci gaba da farautar sauran masu kai hare-hare. Ya kara da cewa, wadannan masu kai hare-hare da mutanen da suka kashe wata malamar addinin Kirista 'yar kasar Italiya a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar a ran 17 ga wata dukansu suna cikin kungiya iri daya.

An labarta cewa, an tayar da boma-boman da ke cikin mata a gaban babban ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Baidoa da ke kudancin kasar a wannan rana, ta haka an kai hari ga ayarin motoci na shugaban wucin gadi Mr. Yusuf, amma Mr. Yusuf ya kubuta daga wannan hari. An ce, mutane 11 sun rasa rayuka a sakamakon wannan harin bom.(Tasallah)