Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 08:55:58    
An fara tattaunawa kan matsalolin da ake fuskanta lokacin da ake raya biranen kasashen Afirka

cri
A ran 18 ga wata a birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, an fara taron koli game da biranen kasashen Afirka na 4. Shugabannin birane fiye da dubu 1 wadanda suka zo daga kasashe daban-daban na Afirka za su tattauna kan yadda za a fuskanci kalubale iri daban-daban da ke gabansu lokacin da ake raya biranen kasashen Afirka a gun wannan taron da za a shafi mako daya ana yinsa.

A gun bikin kaddamar da taron, shugaba Mwai Kibaki na kasar Kenya ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, a cikin hali mai tsanani da ake ciki, ya kamata gwamnatocin wuri na kasashen Afirka su kara karfinsu domin ba da kyawawan hidimomi irin na tushe ga mazaunan birane. Mr. Kibaki ya kuma bayyana cewa, kasar Kenya ta riga ta tsai da kudurin cewa, za ta yi kwaskwarima kan tsarin gwamnatocin wuri na kasar domin gwamnatocin wuri za su iya kara samun ikon daidaita matsalolin da suke fuskanta lokacin da ake raya birane.

Madam Anna Tibaijuka, direkata mai zartaswa ta hukumar tsara shirin unguwannin zama na bil Adam ta M.D.D. ta ce, ana bukatar ba da jagoranci da sarrafa ayyukan raya birane. Idan ba za a iya sarrafa shirin raya birane ba, za a yi barazana ga zaman lafiya da na karkon kasashen Afirka. (Sanusi Chen)