A ran 18 ga wata, shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya sanar da cewa, an soma zaman makoki har na tsawon kwanaki 3 saboda mutuwar manyan jami'ai 12 a cikin hadarin jirgin sama da ya auku a ran 17 ga wata.
A wannan rana, madam Oluremi Oyo, mai ba da taimako ga shugaban kasar Nijeriya kan harkokin watsa labaru da kafofin watsa labaru, ta bayyana cewa, bayan da shugaba Obasanjo wanda ke yin ziyara a kasar Singapore ya sami labarin aukuwar hadarin faduwar jirgin sama, ya nuna bakin ciki da mamaki sosai. Madam Oyo ta tsamo maganar Obasanjo tana, cewar hadarin faduwar jirgin sama "wata babbar masiffa ce ga duk kasar Nijeriya". Madam Oyo ta kara da cewa, shugaba Olusegun Obasanjo ya riga ya gama ziyararsa a kasar Singapore ya koma kasarsa kafin lokacin da aka tsara.
Bugu da kari kuma, Mr. Obasanjo ya nuna jejeto ga iyalan hafsohin da suka rasu a cikin hadari, ya kuma ba da umurnin binciken dalilin da ya haddasa wannan hadari nan da nan. (Sanusi Chen)
|