A ranar 17 ga wata da dare, hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasa na Nijeriya ya bayar da sanarwar cewa, mutane 14 sun mutu a hadarin wani jirgin saman yaki a tsaunuka da ke jihar Benue, a yayin da wasu hudu da suka tsira da rayukansu ma suke bakin mutuwa.
An ce, daga cikin wadanda suka mutu, akwai janar 4 da kuma kanar 4. A ran nan, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Nijeriya, Felix Chukwuma ya ce, jirgin ya fadi ne a kan hanyarsa ta tashi daga birnin Abuja zuwa jihar Cross River da ke kudancin kasar. A kalla dai akwai hafsoshin soja 17 a cikin jirgi. Yanzu ma'aikatar tsaron Nijeriya ta riga ta ba da umurnin yin binciken al'amarin.(Lubabatu)
|