Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-18 18:07:22    
Kabilar Miao

cri

Mutanen kabilar Miao suna da zama a lardin Guizhou da lardin Hunan da lardin Yunnan da lardin Sichuan da jihar Guangxi da lardin Hubei da lardin Hainan da dai sauran yankunan kasar Sin. Amma yawancinsu suna zama a yankunan kudu maso gabashin lardin Guizhou, inda ake hade da lardunan Guizhou da Hunan da Hubei da Sichuan. Bisa binciken da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Miao ya kai fiye da miliyan 8 da dubu 940. Mutanen kabilar Miao suna da yaren Miao, amma yaren da ake magana a yankuna daban suna da bambanci. Tun daga shekarar 1956, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta gayyaci kwararru wadanda suke nazarin yaren Miao da su tsara ko gyara kalmomin Miao da bakaku Latin. Yanzu ana koyar da ilmi a yankunan da mutanen kabilar Miao suke zama da kalmomin Miao.

A cikin dogon lokacin da ya wuce, tattalin arzikin kabilar Miao ya samu ci gaba kadan. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an yi gyare-gyaren dimokuradiyya da kafa gwamnatin dimokuradiyya da yin gyare-gyaren gurguzu a yankunan da kabilar Miao ke zama. Tun daga shekarar 1951, bi da bi ne aka fara kafa gandummomi da yankunan kabilar Miao masu cin gashin kansu. Wannan ya yi amfani sosai wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar yankunan kabilar Miao. A karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, mutanen kabilar Miao sun samu cigaba sosai a fannonin tattalin arziki da al'adu da ilmi da kiwon lafiya a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce. A da, babu masana'antu a yankunan kabilar Miao, amma yanzu an riga an kafa masana'antun zamani da yawa a yankunan kabilar Miao. Zaman rayuwar jama'ar kabilar Miao ya kuma samun kyautatuwa.

A cikin dogon lokacin da ya wuce, mutanen kabilar Miao sun kirkiro adabi da fasahohin zane-zane iri iri ciki har da rubutattun wakoki da tatsuniyoyi iri iri. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Miao suna da sha'awar rera wakoki da raye-raye. Salon raye-rayen da mutanen kabilar Miao suke wasa suna da iri iri.

Sannan kuma, mutanen kabilar Miao suna da fasahar rina da yin tufafi da yin kayayyakin ado. Mutanen kabilar Miao sun riga sun yi amfani da fasahar rina atamfofi har na tsawon shekaru fiye da dubu 1. Yanzu sun iya rinar atamfofi da launuka iri iri, kuma suna fitar da atamfofi da yawa zuwa kasuwannin kasashen waje.

Bugu da kari kuma, jama'ar kabilar Miao sun kirkiro fasahar kiwon lafiya da kansu a cikin dogon lokacin da ya wuce. Sun kuma kirkiro magunguna iri iri da kansu.

A yawancin yankunan da kabilar Miao ke zama, samari da 'yan mata sun iya zaben mata ko miji da kansu cikin 'yanci. A kan shirya wa samari bukukuwa iri iri domin zaben mata ko miji. Bugu da kari kuma, a wasu yankunan kabilar Miao, bayan da wani saurayi da wata mace suka yi aure, ba dole ba ne mace ta yi zama a gidan mijinta. Mai yiyuwa ne mijinta ne ya yi zama a gidanta.(Sanusi Chen)