Wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Tang Jiaxuan ya bayyana a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna cikekken goyon baya ga madam Margaret Chan da ta shiga takarar neman mukamin babbar darektar kungiyar WHO.
Mr.Tang Jiaxuan ya yi wannan furuci ne a yayin da yake ganawa da madam Margaret Chan, wato 'yar takara daga kasar Sin wadda ke neman makamin babbar darektar kungiyar WHO.
Mr.Tang Jiaxuan ya ce, gwamnatin kasar Sin ta nuna cikekken goyon baya ga madam Margaret Chan da ta shiga takarar kuma ta dora muhimmanci sosai a kan batun. Ya kuma yi imani da cewa, sabo da gwanintarta da kuma fasaharta, tabbas ne Madam Margaret Chan za ta ci nasara a wannan mukami.
A nata bangaren kuma, Madam Margaret Chan ta bayyana cewa, za ta ci gaba da kokartawa. Idan ta ci zaben, to, za ta kara ba da taimako ga aikin kiwon lafiya na duniya ba tare da kasala ba.(Lubabatu)
|