Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-18 17:27:00    
Kasar Jamus ta gabatar da shawarar kafa wata tashar tace sinadarin Uranium ta duniya

cri

A ran 18 ga wata, jaridar Handelsblatt ta kasar Jamus ta bayar da wani labari cewa, a cikin 'yan kwanakin baya, ministan harkokin waje na kasar Jamus Frank-walter Steinmeier ya gabatar da shawarar kafa wata tashar tace sinadarin Uranium ta duniya, wadda MDD take sa ido a kanta kuma kasashen duniya suke amfani da ita tare domin su bunkasa aikin makamashin nukiliya na jama'a, da kuma daidaita matsaloli dangane da nukiliya kamar matsalar nukiliya ta kasar Iran.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, Mr Steinmeier ya bayyana cewa, kamata ya yi a kafa irin wannan tasha a kasashe da ba su da nasaba da matsalolin nukiliya, kuma a gudanar da ita bisa sa idon hukumar makamashin nukiliya ta duniya. Kasashen wadanda suke ba da kudi, sai za su sami iznin amfani da wannan tasha, kasasshe kamar Iran da ke da matsalar nukiliya, suna iya yin amfani da irin wannan tasha domin inganta rayuwar jama'a.

Labarin ya ce, babban daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya Mohamed El-Baradei ya riga ya sami wannan shawara, hukumarsa ta riga ta tsara wasu dokoki domin haka.(Danladi)