Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-18 17:25:47    
Sinawa da ke birnin Abidjan suna lami lafiya

cri

Ya zuwa yanzu, mutane 7 sun rasa rayukansu a sakamakon gurbatar muhalli da shara mai guba a birnin Abidjan, babban birnin tattalin arziki na kasar Cote D'ivoire, yawan mutane da suka je ganin likita ya zarce dubu 30. Sinawa da ke birnin Abidjan sun riga sun dauki matakai, a halin yanzu suna lami lafiya.

Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Cote D'ivoire yana cikin yankin da aka zuba sharar mai guba, jami'an ofishin jakadanci 7 ko 8 ciki har da jakada Ma Zhixue sun taba kamuwa da irin wannan guba, amma ba mai tsanani ba. Bayan faruwar al'amarin, ofishin jakadacin ya fadakar da hukumomi da kamfanonin kasar Sin a Cote D'ivoire da Sinawa da ke wurin domin su dauki matakai cikin gaggawa. Sinawa 3 da ke kasar Cote D'ivoire sun taba kamuwa da cutar fatar jiki da dai sauransu, amma a halin yanzu sun sami sauki.

Bisa taimakon da kwararrun kasashen waje suka bayar, gwamnatin kasar Cote D'ivoire ta riga ta fara kawar da shara mai guba a ranar 17 ga wata.(Danladi)