Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-18 17:22:47    
An kiran taron fuska da fuska na hukumomin kafa dokoki na kasashen Sin da Rasha a birnin Ha Erbin na kasar Sin

cri
Ran 18 ga wata a birnin Ha Erbin, birnin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, an shirya taron fuska da fuska na hukumomin kafa dokoki na kasashen Sin da Rasha, a gun taro, kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kwamitin tarrayar kasar Rasha za su yi musayen ra'ayoyinsu kan sakamakon da suka samu wajen kafa dokoki, da sa ido, da kuma karfafa hadin kansu wajen kafa dokoki, domin ingiza bunkasuwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha, da hada kai, da kuma yin cudanya kan al'adu.

Taron wani muhimmin aiki ne na ayyukan "shekarar kasa" da kasashen Sin da Rasha suka shirya. Manyan jami'ain hukumomin kafa dokoki, da kwararru, da kuma jami'ai na shiyya shiyya na kasashen biyu suke halartar taron.

A cikin jawabinsa, Mr. Wu Bangguo, shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, domin zurfafa cudanya da hadin kai, ya kamata hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu su kara kyautatta tushen dokoki na hadin kansu, da aiwatar da ayyukan yin cudanyar kafa dokoki masu amfani, da mai da hankulansu kan ingiza hakikanin hadin kai a fannin tattalin arziki da ciniki, da kuma sa himma domin halartar sauran ayyuka na "shekarar kasa".

Sergei Mironov, shugaban kwamitin tarrayar kasar Rasha yana ganin cewa, ya kamata bangarorin biyu su tsara hakikanan shiri da matakai, da kyautatta dokoki da shari'ar da ke nasaba da hadin kai a tsakanin kasashen Rasha da Sin, ya bayyana imani cewa, sakamako da shawarwarin da za a samu a cikin taron za su yi ma'ana sosai kan zurfafa tsare-tsaren hadin kai da ke kasashen Rasha da Sin. (Bilkisu)