Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-17 18:17:30    
Ana kokari sosai wajen yin amfani da gas da ake samu daga tarin shara a makiyaya na jihar Tibet ta kasar Sin

cri
A jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, ana kokari sosai wajen yin amfani da gas da ake samu daga tarin shara a makiyayya, a wannan shekara, za a kashe kudin Sin Yuan sama da miliyan 16 don gina ramukan tarin shara da yawansu zai kai 2500 don samun gas a makiyayyar jihar nan.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an gina ramukan tarin shara don samun gas bisa gwaji a wasu makiyayya na jihar Tibet.

Ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ta zabi kwararru 50 daga lardin Sichuan da na Liaoning na kasar, ta aika da su zuwa jihar Tibet don ba da taimakonsu wajen gudanar da ayyukan samun gas daga tarin shara, kuma ko wanensu zai horar da manoma da makiyayya da yawansu ya kai goma a jihar. (Halilu)