Ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Cote d'Ivoire sun tabbatar a ranar 15 ga wata cewa, har zuwa yanzu dai, babu Sinawan da suka sha dafi mai tsanani a sakamakon gurbaccewar muhalli da sharar masana'antu masu guba da ya haddasa a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire.
Ma'aikatan sun ce, bayan aukuwar al'amarin, Sinawa masu yawa da ke zaune a birnin Abidjan sun taba jin iska mai guba kwarai, amma har zuwa yanzu, akwai Sinawa uku ne kawai wadanda suka kamu da ciwon kuraje.(Lubabatu)
|