Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 20:55:20    
Gwamnatin Congo Kinshasha tana yaki da mallakar makamai ba bisa doka ba

cri
A ran 15 ga wata, kwamitin tabbatar da zaman lafiya a kasar Congo Kinshasha, lokacin gudanar da babban zabe a kasar ya bayar da wata sanarwa, inda aka sanar da cewa, za a dauki matakai masu zafi domin yin yaki da mallakar matakai ba bisa ka'ida ba don tabbatar da yin zagaye na biyu na babban zaben kasar da za a yi a kasar kafin watan Oktoba cikin zaman lafiya da oda.

Wannan kwamitin ya nuna cewa, wasu mutane suna mallakar makamai ba tare da samun izini ba kuma suna kwace dukiyoyin jama'a, wannan muhimmin dalili ne da ya kawo karuwar aikata laifuffuka.

Wannan kwamiti ya jaddada cewa, duk wanda yake rike da makamai ba tare da samun izini ba, wannan yana nufin cewa ya karya doka. A sa'i daya kuma, kwamitin ya nemi hukumomin tabbatar da zaman lafiya na kasar da su kara daukar matakai domin kama wasu mutane wadanda suke rike da makamai ba tare da samun izini ba. (Sanusi Chen)