Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xin Hua ya bayar, an ce, ya zuwa yanzu, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta riga ta kebe kudin Renminbi yuan kimanin biliyan 7 da miliyan dari 1 daga baitulmali domin ayyukan ba da agaji da ayyukan sake neman bunkasuwa a lardunan Hunan da Fujian da Guangdong da Guangxi kuma da lardin Sichuan wadanda suka sha fama da bala'u daga indallahi.
Ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayar da wannan labari a ran 15 ga wata.
An bayar da labari cewa, yanzu, muhimman ayyukan ba da agaji a wurare da suka sha fama da bala'u daga indallahi sun hada da inganta rayuwar jama'a da sake masu gidajen kwana.
Kwanan baya, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar ta bayyana cewa, za a tabbatar da magance matsalar rashin wurin kwana ga wadanda bala'u suka rutsa da su kafin lokacin hunturu. A watan Nuwamba mai zuwa, hukumomin da abin ya shafa za su yi kira ga al'ummar kasar da su ba da taimakon kudi da kayayyaki ga mutanen da ke sha fama da bala'u. (Sanusi Chen)
|