|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-09-15 16:25:59
|
Rukunin Citi Group ya ba da kyautar kudi fiye da Yuan miliyan daya domin taimaka wa yaran da suka dakatar da karatu sabo da talauci
cri
A ran 14 ga wata a nan birnin Beijing, an yi wani bikin ba da taimako ga makarantu, a gun bikin rukunin Citi Group ya yi shirin ba da kyautar kudi har Yuan miliyan daya da dubu 168 domin taimaka wa yaran da suka dakatar da karatu sabo da talauci.
An yi wannna aiki ne domin taimaka wa yara masu fama da talauci da yawansu ya kai 120 na lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin da suka dakatar da karatu sabo da talauci don su samun ilmin a makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 ta hanyar yin amfani da moriyar tattalin arziki da aka samu bayan da aka dasa bishiyoyi. (Umaru)
|
|
|