Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 16:18:28    
Za a kawar da manyan abubuwa iri biyu da ke lalata malfal duniya daga kasar Sin kwata-kwata kafin karshen watan Yuli na shekarar badi

cri
Kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen kawar da manyan abubuwa iri biyu wato CFCs da Halon a Turanci wadanda ke lalata malfal duniya daga kasar Sin kwata-kwata, kafin ran 1 ga watan Yuli na shekarar badi.

Ran 16 ga wata ranar duniya a 12 ce ga kare malfal duniya. A ran 15 ga wata, kasar Sin ta yi taron tunawa da ranar a birnin Changchun da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kuma ta bayar da wannan kuduri da ta tsai da.

An ruwaito cewa, tun bayan da kasar Sin ta rabbata hannu kan "yarjejeniyar Montreal a kan abubuwan da ke lalata malfal duniya" a shekarar 1991, sai sannu a hankali gwamnatin kasar Sin ta tsara manufofinta game da gaggauta kawar da abubuwa da ke lalata malfal duniya daga kasar Sin, kuma ta kokarta wajen samun sauran kayayyaki da ke maye gurbin wadannan abubuwa. Bisa ka'idojin yarjejeniyar, ya kamata, tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2010, kasar Sin ta daina fitar da abubuwan nan iri biyu wato CFCs da Halon kwata-kwata da kuma daina yin amfani da su. Amma kasar Sin za ta kammala yin haka kafin lokacin ya cika wato a ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2007. (Halilu)