Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-15 16:13:01    
Gudummowar da kasar Sin take bai wa Afrika sahihiya ce kuma babu son zuciya a ciki a cewar shugabannin kungiyoyin 'yan kwadago na Afrika

cri

A ran 13 ga watan da muke ciki, a nan birnin Beijing, wassu shugabannin kungiyoyin 'yan kwadago na kasashen Afrika dake yin ziyara yanzu a kasar Sin sun yi farin ciki da fadin, cewa lallai gudummowar da gwamnatin kasar Sin take samar wa kasashen Afrika sahihiya ce kuma babu son kai a ciki. Labuddah, kasashen Afrika da jama'arsu sun samu moriya mai tsoka saboda da gwamnatin kasar Sin ta rage da kuma cire basussukan da suka ci da kuma nuna musu kyakkyawan gatanci wajen bada rancen kudi.

Shugabanni 26 na kungiyoyin 'yan kwadago na kasashe 17 masu amfani da harshen Turanci daga Nahiyar Afrika sun zo nan kasar Sin domin halartar ' Taron kara wa juna sani tsakanin shugabannin kungiyoyin 'yan kwadago na kasashe masu yaren Turanci na Afrika', wanda aka bude shi a ran 12 ga watan da muke ciki a nan Beijing. Wadannan shugabanni sun yi shawarwari da kuma nazari a fannoni da dama tare da jami'an da abun ya shafa na kungiyoyin 'yan kwadago na kasar Sin game da batutuwan ' yunkurin bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya bai daya da kuma hadin gwiwar da ake yi tsakanin kungiyoyin 'yan kwadago na kasar Sin da kasashen Afrika'.

Shugaban hadaddiyar kungiyar ma'aikatan duk kasar Namibia wato Mr. Avus Mohe ya fada wa manema labaru na Kamfanin Dillancin Labaru na Xinhua, cewa gudummowar da gwamnatin kasar Sin take samar wa kasashen Afrika ta sha bamban da ta kasashe masu hannu da shuni na Yamma. Gwamnatin kasar Sin takan bada taimako wajen raya muhimman ayyuka da kuma yin tallafin kudi ga kasashen Afrika daidai bisa bukatunsu na hakika. Yansu, ana yin aikin gina babban ginin gwamnatin Namibia a birnin Windhoek, hedkwatar kasar bisa taimakon da gwamnatin kasar Sin ta bayar.

Mun sami labarin, cewa gwamnatin kasar Sin ta soma bai wa kasashen Afrika gudummowa ne a shekarar 1950 na karnin da ya gabata. Ba da taimakon kayayyaki, wata muhimmiyar hanya ce da aka bi a wancan lokaci. Amma a cikin shekaru sama da 50 da suka shige, gwamnatin kasar Sin takan samar da gudummowa ta hanyoyi da dama. Alal misali: gwamnati kasar Sin ta bayar wa kasasshen Afrika da taimakon gina ayyuka kusan 900 na bunkasa tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma; Bugu da kari kuma, ta aika likitoci da nas-nas da yawansu ya kai 16,000 zuwa kasashe 47 na Nahiyar Afrika; Kazalika, ta samar da alawas din gwamnati ga kasashe 50 na Afrika; Dadin dadawa, ta tura sojoji da hafsoshi fiye da 3,000 bi da bi zuwa Nahiyar Afrika domin aiwatar da dawainiyar kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta dora mata.

Mr. Mohe ya kuma furta, cewa ' Kasar Sin kasa ce ta farko da ta samar mana da taimakon kudi da na kayayyaki, kuma har kullum muna daukarta a kan ita ce 'yar-uwanmu'.

A 'yan shekarun baya, an samu yalwatuwa da saurin gaske tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya.

Mr. Gideon Yoke, mataimakin babban sakataren kungiyar 'yan kwadago ta Afrika ta Kudu ya yi jawabi a gun taron kara wa juna sani, inda ya yi fatan masu zuba jari na kasar Sin za su kara gabatar wa kasashen taimako a fannin musayar fasahohi da yin horo a fannin fasaha, ta yadda kasashen Afrika za su gudanar da ayyukan kawo albarka a yankunansu.

Yanzu, gina muhimman ayyukan gini da kuma raya albarkatun leburori sun riga sun zama muhimman fannoni na yunkurin daukaka ci gaban hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya. An labarta, cewa akasarin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a ketare yana cikin Nahiyar Afrika, wanda ya hada da fannin danyun kayayyaki, da makamashi, da zirga-zirga ,da kiwon lafiya ,da na riga-kafi da shawo kan cututtuka da dai sauran fannoni. ( Sani Wang )