Nan da 'yan shekaru masu zuwa, kasar Sin za ta sha wahala sosai wajen samar da guraben ayyukan yi, yawan guraben ayyukan yi da ake karancinsu zai kai miliyan 13 a ko wace shekara a birane da garuruwa na kasar.
Wakilin gidan rediyon kasar Sin ya sami wannan labari ne daga ma'aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman jama'a ta kasar Sin a ranar 15 ga wata.
An ruwaito cewa, nan da 'yan shekaru masu zuwa, yawan mutane da ke neman aikin yi zai wuce miliyan 24 a ko wace shekara a birane da garuruwa na kasar Sin. Amma yawan sabbin guraben ayyukan yi da za a samar zai kai miliyan 11 kawai. Ka zalika akwai manoma na kasar da yawansu ya kai kimanin miliyan 100 su ma za su nemi ayyukan yi. (Halilu)
|